A taron manema labaran da suka kira da yammacin jiya Talata a ofishin Moden Lumana dake unguwar Zabarkan ta birnin Yamai, shugabanin kwamitin kolin madugar jam’iyun hamayya ta tsohon Firai minister Hama Amadou sun sanar da yanke shawarar baiwa dan takarar jam’iyar RDR Canji Alhaji Mahaman Ousman goyon baya a zaben shugaban na ranar 27 ga watan Disamba.
Saboda haka ne kuma shugabannin suka bukaci ‘yayan Lumana Afrika su ba tsohon shugaban kasa kur’un su a ranar Lahdin dake tafe. Maman Sani Malan Mahaman shine babban magatakardan wannan jam’iya wanda ya yi karin haske a kan wannan mataki.
Ya ce “mun fadawa duk wani mai kishin kasar Nijer dake so ya ga Nijer ta kasacen cikin kwanciyar hankali da zama lafiya, ya mika kuri’ar sa ga tsohon shugaban a matsayin dan takaran da Lumana ta amince da shi”.
Da yake bayyana matsayinsa a game da wannan mataki tsohon shugaban kasar ta Nijer ya yi farin ciki da samun goyon bayan mutanen da ya kira abokan tafiya na shekara da shekaru.
Ya ce “na tabbata wannan goyon baya da na samu daga Hama Amadou da jami’iayr sa ta Lumana ba sabon abu bane saboda mun taba aiki tare kana sun yi tunani mai zurfi da suka yanke wannan shawara cewa ni ne zan kawo canji”.
Jam’iyar ta Moden Lumana wacce ke sahun jam’iyu kimanin 11 da kotun tsarin mulkin kasa ta yi watsi da takardun mutanen da suka tsayar a matsayin ‘yan takarar shugaban kasa ta yi nasarar tsayar da ‘yan takarar zaben ‘yan majalisar dokokin kasa da zai gudana a rana daya da na shugaban kasa saboda haka uwar jam’iyar ke tunatar da ‘yayanta a kan wannan kudiri.
Da ma dai a washegarin bayyanar matakin da ya hana masa shiga zabe, Hama Amadou ya sanar da cewa ya rungumi kaddara amma kuma ya kira magoya bayan jam’iyar sa ta Moden Lumana su kwana da shirin halartar runfunar zabe domin kadawa dan takarar da ya cika sharudan da shi da mukarrabansa suka gindaya .
Ga dai rahoton Souley Moumouni Barma daga birnin Yamai:
Your browser doesn’t support HTML5
Karin bayani akan: Hama Amadou, Najeriya, da Nigeria.