Kungiyoyin likitoci, kwararru a fannin magani da likitocin hakori ne suka rubuta a shafinsu na twitter a yammacin ranar Lahadi cewa babu wani mataki da aka dauka akan korafe-korafen da suka gabatar watanni 8 da suka gabata.
“Gwamnatin Kenya ta yi watsi da batun lafiya da walwalar jami’an lafiya, da kariyarsu,” a cewar kungiyar ma’aikatan. Babu tanadin insurar asibiti, da wasu tallafe-tallafen ma’aikata. Tabbas wannan ya kawo cikas sosai a yakin da ake yi da annobar COVID-19 a kasar da ke fuskantar karancin likitoci.
Kasar Kenya ta bada rahoton samun adadin masu kamuwa da cutar COVID-19 dari uku da arba'in da tara ranar Lahadi 20 ga watan Disamba, da mace-mace 6, abinda ya sa gaba dayan adadin masu cutar da aka samu a kasar yanzu ya kai 94,500, sai kuma mace-mace 1,639 a cewar ma’aikatar lafiyar Kenya.