An hambarar da dadadden shugaban kasar ne a wani juyin mulkin soji a cikin watan Afrilu a shekarar 2019, bayan gagaruman zanga zanga a kan tabarbarewar tattalin arziki da kuma mulkin kama karya da Bashir ya yi a mulkin sa na shekaru 30.
Galibin ‘yan Sudan sun bayyana rashin jin dadin su a kan abin da suka kira tafiyar hawainiya ko kuma sauya tafiya da ake gani karkashin gwamnatin wucin gadi da ta sha fama wurin magance matsalolin tattalin arziki a lokaci da kasar take cikin rikici.
An kafa gwamnatin ne a karkashin yarjejeniyar shekaru uku ta raba madafun iko tsakanin sojoji da kundiyoyin fararen hula, da zummar zata shirya zaben gaskiya na shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki.
Telbijin gwamnatin Sudan ta nuna hoton dubban masu zanga zanga sun taru a wajen fadar shugaban kasa a birnin Khartoum, inda hukumar zartarwar kasar ke gudanar da ayyukanta karkashin gwamnatin hadaka tsakanin sojoji da fararen hula.
An kashe daruruwan ‘yan Sudan a cikin zanga zanga kafi hambarar da tsohon shugaban kasar da ma bayan da ya sauka daga karagar mulki.
Wasu da dama suna kira ga rusar da majalisar dokoki da ta zartarwar da kuma gwamnatin hadakar.