Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Zaben Nijar


ZABEN NIJAR
ZABEN NIJAR

Jamhuriyyar Nijar kasa ce da ke yammacin Afirka wacce ke bin tafarkin dimokradiyya. Tana bin tsarin shugabanci wanda iko da umurni ke gudana daga gwamnatin tsakiya. 

A ranar 27 ga watan Disamba za a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisa.

Shugaba Mahamdou Issoufou na jam’iyyar PNDS shi ne shugaba mai ci, wanda wa’adinsa zai kare a farkon watan Afrilun badi.

Jam’iyyyun Siyasa:

Nijar na da jam’iyyun siyasa akalla 266 amma ‘yan takara 30 ne suke neman shugabancin kasar ciki har da wadanda ke zaman kansu (wato wadanda suke takara babu jam’iyya).

Daga cikin wadannan jam’iyyun akwai MNSD Nassara, Moden Lumana, PNDS Tarayya (mai mulki,) RANAA, PJP, Amen Amin, Nigerena, SDR- Sabuwa, UNPP, MPR da dai sauransu.

‘Yan Takarar Shugaban Kasa:

A zaben nan na 2020, ‘yan takara 30 ne suke neman shugabancin Nijar, daga cikinsu akwai Oumarou Abdurahamane, Amadou Issoufou Saidou, Ibrahim Yacoubou, Mohamed Bazoum, Albade Bouba, Salou Djibou, Hamidou Mamadou Abdou, da Seini Oumarou.

Sauran sun hada da Omar Hamidou Tchiana, Elh. Dr. Abdallahi Souleymane, Kane Kadaoure Habibou, da dai sauransu.

‘Yan Takara Da Ake Ganin Za Su Taka Rawar Gani:

Binciken da VOA ta gudanar da kuma yadda al’amura ke gudana, ‘yan takarar da hankali ya fi karkata akansu, sun hada da na jam’iyyar PNDS mai mulki Mohamed Bazoum, Albade Abouba na MPR da Seini Oumarou na MNSD Nassara.

Babbar Jam’iyyar Adawa:

Babbar jam’iyyar adawa a wannan zabe ita ce Moden Lumana, wacce har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto ba ta da dan takarar shugaban kasa.

Kotun Tsarin Kundin Mulkin Jamhuriyar Nijar ta soke takarar Hama Amadou, wanda tsohon kakakin majalisa ne kuma tsohon Firai Minista, saboda badakalar da aka same shi da laifi ta safarar jarirai daga Najeriya.

Amadou ya kwashe watannin kusan tara a kurkuku bayan da aka same shi da laifi aka kuma yanke masa hukunci a shekarar 2017.

Masu fashin baki da dama na ganin zaben ba zai yi armashi ba lura da cewa babu tsayayyen dan takara na adawa a zaben shugaban kasar – abin da ya sa wasu ke ganin mai yiwuwa Bazoum ya ci karensa ba babbaka.

Kalubalen Bazoum:

Babban kalubale da Mohamed Bazoum ke fuskanta shi ne batun da wasu suka tayar na cewa shi ba asalin dan Nijar ba ne, lamarin da ya sa wata gamayyar ‘yan takarar shugaban kasa ta shigar da shi kara kan a janye takararsa.

Amma kotun ta yi watsi da wannan kara kusan makonni biyu da suka gabata.

A makon da ya gabata, dan takarar jam’iyyar PJP, Salou Djibou ya sake tayar da batun inda ya yi barazanar cewa zai garzaya kotu domin a hana Bazoum takara.

Shi dai Bazoum ya masunta wannan ikrari da ke cewa shi ba dan kasa ba ne.

Adadin Kuri’un Da Ake Bukata Dan Takara Ya Samu Kafin Lashe Zabe:

A zaben Nijar, ana bukatar dan takara ya samu kashi 51 na kuri’un da aka kada kafin a ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zabe.

Idan aka samu akasin hakan, sai an je zagaye na biyu, inda akan zabi ‘yan takara biyu da suka fi yawan kuri’u domin karawa a zagayen.

Misali idan dan takara A ya samu kashi 40 na kuri’un da aka kada, sai dan takara B ya samu kashi 35, sauran ‘yan takarar kuma suka samu kason da ya gaza na A da B – hakan na nufin A da B ne za su je zagaye na biyu don karawa. Sauran kuma duk za a zubar da su.

Ranar 21 ga watan Fabarairu ce ranar da aka tsayar a matsayin wadda za a yi zabe a zagaye na biyu.

Dalilin Da Ya Sa Ake Cewa Zaben “2020 Da 2021”:

A tsarin zaben Nijar, a duk watan Disamba ake gudanar da babban zaben kasar, akan kuma hada shekara biyu ko da za a je zagaye na biyu.

Misali, kamar yadda za a yi zaben a watan Disambar shekarar 2020, idan har aka gaza samun dan takara da ya samu kashi 51 na kuri’un da aka kada, dole sai an shiga shekara 2021 domin a je zagaye na biyu.

A ranar 21 ga watan Fabarairu ake fatan yin zaben a zagaye na biyu idan har aka gaza samun dan takarar da ya samu kashi 51.

Majalisar Dokokin Nijar:

Majalisar Dokokin Nijar, na da kujeru 171, kuma ba kamar yadda ake gani a wasu kasashe irinsu Najeriya da ke da majalisa biyu ba – wato ta wakilai da ta dattawa, a Nijar majalisa daya suke da ita, wacce ke samun wakilai daga jihohi takwas da ke kasar.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG