Ministocin Harkokin Wajen Kasashen Sahel Za Su Hada Kai A Taron MDD

Shugabannin kasashen Mali, Nijar da Burkino Faso - AES

A karshen taron da suka gudanar a birnin Bamako ministocin harakokin wajen kasashen sahel da suka hada da Nijar, Mali da Burkina Faso masu fama da matsaloli iri daya sun sanar cewa sun cimma matsaya domin yin magana da yawu guda a taron MDD na shekara shekara.

Kasashen AES da suka hada da Nijar, Mali da Burkina Faso za su hada kai a kan dukkan batutuwan da za a gabatar a yayin wannan zama da zai tattara shugabannin duniya a karshen watan nan na satumba a birnin New York.

Tsaro na kan gaba a fannonin da Nijar, Mali da Burkina Faso ke kokarin samar wa mafita ganin yadda kasashen uku da ke karkashin mulkin soja ke ci gaba da fuskantar munanan hare-haren ta’addanci da na ‘yan bindiga.

Sannan Sabuwar alkiblar da suka dosa mataki ne da suka fahimci cewa ya zama wajibi su kasance tsintsiya madaurinki daya a fannin diflomasiya, mafarin wannan taro na wuni biyu.

Karamako Jean Marie Traore ministan harakokin wajen Burkina Faso, yaa ce ‘’a matsayinsu na ministocin harakokin waje sun hadu ne domin bitar ayyukan hadin gwiwar da kasashen suka gudanar.

"Kuma zaman na gudana ne a jajibirin babban taron MDD lokaci ne da ya dace su tattauna a tsakaninsu kan batutuwan da za a tabo a birnin New York don ganin an yi tafiya guda kuma a yi magana da yawu guda.’’ a cewarsa.

Ministan harakokin wajen Nijar Bakari Yaou Sangare ya yaba da yadda kasashen uku ke matukar dasawa da juna a fannin dflomasiya.

Ya ce ‘’tun daga ranar da Mali da Burkina Faso suka bayyana cewa afkawa Nijar da yaki tamkar su ne aka farwa ba kasar da ta taba yin wani abu ita kadai, komai ya taso koma wace irin magana ce komai mahimmancinta kasashen na tuntubar juna su yi shawara a kai. Wannan ya sa dukkan nasarorin da ake samu a fagen daga abu ne da ke da nasaba da ayyukan hadin gwiwar dakarun kasashen uku’’.

Mali da Nijar wadanda suka karfafa hulda da kasar Rasha bayan raba gari da kasashen yammacin duniya sun yanke hulda da Ukraine a watan Agustan 2024 saboda abinda suka kira goyon bayan da take bai wa ‘yan ta’addan yankin Sahel sanadiyar kisan wasu sojojin Mali da na kamfanin Wagner a arewacin Mali, lamarin da ya sa kasashen kawancen na AES shigar da kara a gaban MDD.

Taron na Bamako ya kara jaddada matsayin kasashe na AES dangane da yadda suke kallon hukumomin Kiev abin da ke nufin wannan batu na daga cikin abubuwan da Nijar, Mali da Burkina Faso za su nemi ganin an tafka mahawwara kansu a taron na MDD na bana.

Kawo yanzu dai Ukraine ba ta taba cewa kala ba dangane da zargin alakarta da ‘yan ta’addan sahel.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Ministocin Harakokin Wajen Kasashen Sahel Za Su Hada Kai A Taron MDD.MP3