A gefe guda kuma za a gudanar da wani taron koli gobe Lahadi a Najeriya inda shugabannin sauran kasashe mambobin kungiyar tattalin arzikin yankin ta ECOWAS za su hallara.
Taron kolin da ake yi yau Asabar a Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar, zai kasance karo na farko tsakanin shugabannin sojojin sabuwar kungiyar hadin kan yankin Sahel wato Alliance of Sahel States ko kuma AES.
Mali, Burkina Faso da Nijar su ne suka kafa yarjejeniyar kare juna a watan Satumba, wandanda suka bar babbar kungiyar ECOWAS a cikin watan Janairu.
Ficewar su daga ECOWAS, wani bangaren ya samo asali ne daga zargin da suke yi cewa Paris tana yiwa kungiyar katsalandan kana bata bada taimakon da ya kamata a yaki da masu ikirarin yakin jihadi.
Ficewar tasa kasashen uku sun janye kansu daga Faransa da ta yi musu mulkin mallaka, suka kori sojojin Faransa masu yaki da masu ikirarin jihadin kana suka juya zuwa ga kasashen da suke kira da aminan gaskiya, da suka hada da Rasha da Turkiya da kuma Iran.
Idan aka yi la’akari da munanan tashe-tashen hankula na ‘yan jihadi da kasashen uku ke fuskanta, “yakin da ta’addanci” da “karfafa hadin gwiwa” za su kasance kan ajandar taron kolin na yau Asabar, a cewar fadar shugaban kasar Burkina Faso.
Taron kolin da za a gudanar gobe Lahadi a Abuja zai ba shugabanni a kasashen ECOWAS damar tattaunawa a kan irin alaka da za su kulla da kungiyar ta AES.
Bayan wasu tarurrukan da suke yi tsakanin kasashe biyu, shugabannin uku na yankin Sahel sun yi taro a karon farko tun bayan da suka hau karagar mulki ta hanyar juyin mulki tsakanin shekarar 2020 zuwa 2023.
Dandalin Mu Tattauna