Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar, Mali Da Burkina Faso Na Tattaunawa Kan Matsalolin Tsaro A Iyakokinsu


Mahalarta taro kan tsaro daga Mali, Nijar da Burkina Faso a Yamai
Mahalarta taro kan tsaro daga Mali, Nijar da Burkina Faso a Yamai

Za a  kammala taron a yammacin Juma’a 24 ga watan Maris inda a karshe mahalartan za su tsayar da shawarwarin da za su gabatar da su wa gwamnatocin kasashen uku.

Jami’an kwamitin tsaron hukumar hadin gwiwar kasashen yankin Liptako Gourma (ALG) wadanda suka hada da Burkina Faso, Mali da Nijar na gudanar da taro a birnin Yamai da nufin tattauna hanyoyin tunkarar matsalolin tsaron da ke kara ta’azzara musamman ta bangaren da wadannan kasashe ke da iyaka daya.

Sama da shekaru 50 kenan da kasashen uku suka kafa kungiyar ‘Liptako Gourma’ da zummar karfafa hulda da dangantaka a tsakanin al’umomin kasashen uku da ke makwaftaka ta yankin Liptako.

Sai dai yanayin tabarbarewar tsaron da aka shiga a ’yan shekarun nan ya sa gwamnatin kasashen canza wa kungiyar matsayi zuwa hukumar “Autorite du Liptako Gourma” (ALG) inda aka fadada ayyukanta ga fannin tsaro a shekarar 2017.

Hakan ne mafarin jami’an ma’aikatar tsaro da na cikin gidan kasashen uku suke haduwa lokaci zuwa lokaci don kara jan damarar yaki…

Mai ba Ministan tsaron Burkina Faso shawara Kanal Amadou Dabre na mai ganin bukatar canza salo a fagen daga, tsarin da ya ce wajibi ne kowacce daga cikin kasashen uku ta yi la’akkari da shi.

Wannan ya sa wakilin Mali mashawarci a ofishin ministan tsaron kasar ta Mali, Kanal Ishak Goita, ke cewa taron na Yamai dama ce ta jan hankulan ‘yan siyasar kasashen na yankin Liptako su mayar da bambance-bambance share daya.

Yawaitar bindigogi a hannun jama’a na daga cikin manyan matsalolin da aka gano cewa suna kara rikita al’amura a yankin na Liptako Gourma saboda haka taron zai nazarci hanyoyin tunkarar wannan kalubale.

Za a kammala taron a yammacin Juma’a 24 ga watan Maris inda a karshe mahalartan za su tsayar da shawarwarin da za su gabatar da su wa gwamnatocin kasashen uku.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:

Nijar, Mali Da Burkina Faso Na Tattaunawa Kan Matsalolin Tsaro A Iyakokinsu - 3'30"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:31 0:00

XS
SM
MD
LG