Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar, Mali Da Burkina Faso Za Su Hada Kai Wajen Yakar 'Yan ta'adda


Taron NBM - Ministocin Hadin Gwiwa Na Nijar, Burkino Faso Da Mali Don Magance Matsalar ‘Yan Ta’adda A Yankin Sahel
Taron NBM - Ministocin Hadin Gwiwa Na Nijar, Burkino Faso Da Mali Don Magance Matsalar ‘Yan Ta’adda A Yankin Sahel

Gwamnatin rikon kwaryar Jamhuriyar Nijar ta amince wa dakarun kasashen Mali da Burkina Faso su shiga kasar don bin sawun ‘yan ta’adda a duk lokacin da bukatar hakan ta taso a ci gaba da karfafa matakan yaki da kungiyoyin jihadin da suka addabi yankin Sahel.

NIAMEY, NIGER - A karshen wata tattaunawar da ta hada Ministan harkokin wajen Nijar Bakari Yaou Sangare da takwarorinsa na Mali Abdoulaye Diop da ta Burkina Faso, Olovia Rouamba a albarakcin ziyarar wuni daya da suka gudanar a birnin Yamai, kasashen uku sun kara jaddada aniyar karfafa matakan hadin gwiwa a fannin tsaro kamar yadda aka bayyana a sanarwar karshen taro wacce sakataren ma’aikatar harakokin wajen Nijar Oumarou Ibrahim Sidi ya gabatar.

Oumarou ya ce a fannin tsaro ministocin uku sun tabo matsalolin ta’addanci da na masu yada akidar tsauraran ra’ayi a yankin Sahel da Afrika ta Yamma musamman a kasashen nan uku makwaftan juna.

Sun jaddada aniyar hada karfi don murkushe wadanan masifu da ake fuskanta shekara da shekaru a wannan yanki wanda kuma ke tarnaki ga ayyukan ci gaban al’umma.

Sun kuma nanata bukatar karfafa tsarin musanyar bayanai da ayyukan sintiri na hadin guiwa don fatattakar kungiyoyin ta’addanci. Haka kuma kasashen nan uku sun amince su bai wa juna daukin soja a duk lokacin da aka fuskanci wani farmaki daga waje ko wani harin ta’addanci.

Domin cimma nasara a yunkurin da suka sa gaba wadanan kasashe sun yanke shawarar kafa wata cibiyar tuntubar juna wacce a karkashinta za su tafiyar da ayyukan hadin guiwa a kokarin magance dukkan kalubalen da ka iya tasowa.

Haka kuma a cewarsu, kofa na bude ga dukkan wata kasar da ke fatan shiga wannan tafiya ta neman zaman lafiyar tsaron harkokin kudade da tattalin arziki. Dalilin da kenan suka kudiri aniyar kafa wata sakatariyar hadin guiwa a cewar wannan sanarwa.

Taron Ministocin ya yaba da wasu dokoki biyu da Shugaban Majlaissar CNSP Janar Abdourahamane Tchiani ya saka wa hannu a jiya Alhamis wadanda ke bai wa sojojin Mali da na Burkina Faso izinin tsallaka iyakar Nijar a duk lokacin da aka fuskanci wata barazanar tsaro.

Da ma dai masana sun sha gargadin gwamnatocin kasashen Sahel akan maganar hadin kai don tunkarar kalubalen da ya addabi wannan yanki yau shekaru a kalla 10 ke nan a cewar Dr. Seidik Abba mai sharhi akan lamuran tsaro.

Tsamin dangantakar da aka fuskanta a tsakanin Nijar da kasashen Mali da Burkina Faso sakamakon juyin mulkin da soja suka yi a wadanan kasashe biyu ya haifar da zaman marina a tsakaninsu haka kuma sabon yanayin siyasar da yankin ya tsinci kansa ya ruguza Kungiyar G5 Sahel wacce ainihi ta kudirtawa kanta yaki da ‘yan ta’ada a illahirin kasashe 5 mambobinta.

Saurari ciakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

 Nijar Ta Amince Wa Mali Da Burkina Faso Shiga Kasar Don Fatattakar 'Yan Ta'adda .mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG