Matasan Kirista Sun Fara Gudanar Da Taron Kasa a Jamhuriyar Nijar

Taron matasan Kirista a Jamhuriyar Nijar

A jamhuriyar Nijar matasan kirista na Majami’ar Evangelique sun fara gudanar da taronsu na kasa karo na 45 a birnin Yamai

Matasan na gudanar da taron ne da nufin tattaunawa akan irin gudunmawar da ya kamata su bayar domin bunkasa tattalin arzikin kasa da ci gaban al’umma.

Jan hakalin matasan Kirista akan maganar gwada kyawawan dabi’u a duk inda suka tsinci kansu na matsayin wani bangare na abubuwan dake kunshe cikin ajandar taron kamar yadda Adamu Maidaji memba a kwamitin tsare tsare ya fada.

Tsatsauran ra’ayin addini na daga cikin matsalolin da aka yi imanin cewa suna kan gaban dalilan dake haddasa fitintinun da ake fama da su a yau a duniya, mafari kenan da taron na Yamai ke son ganar da matasa illar wannan halayya.

Domin bayar da misali akan mahimmancin kawar da bambance-bambancen dake da nasaba da dalilan addini kungiyar matasan krista ta gayyato wasu matasan musulmi domin halartar bikin bude wannan taro.

A shekarar 1973 aka kirkiro da wannan taro na camp des jeunes da zummar karfafa dankon zumunci tsakannin matasa majami’ar ANGELIKAN EERN, dalilin taron na tsawon kwanaki shida mahalartan ke saran gudanar da wasu aiyukan jin kai da suka hada da ziyartar firsinoni bayar da gudunmawar jini a Asibiti, sai kuma aiyukan dashen itace a wata unguwar birnin Yamai.

Domin karin bayani saurari rahotan Sule Muminu Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

Matasan Kirista Sun Fara Gudanar Da Taron Kasa a Jamhuriyar Nijar - 3'13"