Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin Bayan Zabe Ya Lakume Rayuka Biyu A Zimbabwe


Masu zanga zanga a Zimbabwe
Masu zanga zanga a Zimbabwe

Zanga zangar da ya barke bayan zaben da aka gudanar a Zimbabwe ya hallaka rayuka biyu saboda jinkirin da aka samu wajen bayyana sakamakon zaben

An harbe mutane 2 a babban birnin Zimbabwe a jiya Laraba, wannan ko ya faru a lokacin da jami’an tsaro suka yi arangama da masu zanga-zanga wadanda ke bukatar a gaggauta bayyanan sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar.

Biyo bayan wannan fadan ne rundunar ‘yan sandar kasar ta bukaci gudun mowar soja da su taimaka domin a samar da zaman lafiya a Harare fadar gwamnatin kasar.

Yayin da ‘yan kasar ke dakon sakamakon zaben shugaban kasa daga ranar littinin data gabata, wanda shine irin na farko a cikin shekaru 38 da aka gudanar ba tare da sunan tsohon shugaban kasar ba Robert Mugaba a takadar jefa kuri’a.

Wannan tsaikon ne yasa ‘yan adawa cewa shugaban su Nelson Chamisa shine yayi galaba akan shugaba Emerson Mnangagwa.

Tsohon Prime Ministan kasar Habasha Hailemariam Desalegn shine ya jagoranci tawagar kungiyar tarayyar Amfrica data sa ido a zaben. Ga kuma abinda yake cewa

"Mun bukaci hukumar zaben kasar ta Zimbabwe da ta kokarta ta ga cewa ta samar da sakamakon sauran abinda ake jira kan lokaci kamar yadda dokar kasar ta shinfida , haka kuma muna kira ga masu ruwa datsaki a wannan zaben musammam ma shugabannin jamiyyun siyasa da magoya bayan su da suci gaba da nuna halin dattaku, tare da kaurace wa duk wani abu da ka iya kawo wa tsarin cikas ko kuma koma baya ga zaman lafiyar kasar".

Shugaba Mnangagwa wanda jamiyyarsa ta ZANU -PF ke kan gaba a sakamakon da aka riga aka fidda ya bukaci jama'ar kasar su zauna lafiya, kuma ya fadi hakan ne a shafin sa na Twitter.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG