Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Batun Tsaro Ya Mamaye Jawabin Shugaban Niger A Ranar Tunawa Da Samun 'Yanci


Shugaban Niger Mahamadou Issoufou
Shugaban Niger Mahamadou Issoufou

Shugaban kasar Niger Mahamadou Issoufou ya yiwa al’umar kasar jawabi a albarkacin zagayowar ranar cika shekaru 58 da kasar ta samu ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka na kasar Faransa.

Batun tsaro a yankin sahel da yankin tafkin Cadi na kan gaba a batutuwan da suka mamaye jawabin shugaba Issoufou, wanda ya tabbatar cewa rundunonin hadin gwuiwar da kasashen da abin ya shafa suka kafa suna samun nasara sosai a yakin da suke kafsawa da ‘yan ta’adda.

Wannan shugaba Issoufou yace ya karya lagon Boko Haram, sai dai har yanzu da sauran rina a kaba dalili kenan da ya bukaci kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya amincewa bukatun kasashen G5 na SAHEL, akan maganar samun cikakken goyon bayan kasashen duniya a wannan gagarumin yaki…

Domin tabbatarwa dakarun Niger gamsuwa da jajircewarsu a fagen daga, shugaba Mahamadou Issoufou ya umurci shuwagabanin rundunar mayakan kasar su ware kaso na musamman ga ‘yayan jami’an tsaron da suka kwanta dama ko suka samu nakasa a fagen-daga, a yayin aiyukan daukar sabbin sojoji.Sannan yace ya umurci gwamnatinsa ta rubanya kudaden fanshon sojojin da suka rasu a fagen yaki, ta yadda magadansu zasu amfana…

Shugaban kasar Niger ya bayyana cewa zabubukan 2021 na da muhimmanci saboda haka yace ya umurci gwamnati ta baiwa hukumar zaben kasar dukkan abubuwan da take bukata domin shirya sahihin zabe da zai baiwa kowa damar shiga a dama da shi. Saboda haka ya yi kiran jam’iyyun siyasa kadda su maida kansu saniyar ware a aiyyukan da aka kadammar domin hada kundin rajista.

Haka nan shugaba Muhamadou Issoufou ya yi tur da rikicin kabilancin da ake fama da shi akan iyakar Niger da Mali.

Yayinda ya nuna farin ciki akan yanayin da damunar bana, shugaban ya bayyana takaicinsa a game da sakamakon jarabawar BAC da BREVET da aka gudanar a watannin Yuni da Yulin da suka gabata. Yana mai cewa faduwar dalibai a wannan jarabawa wani abu ne dake da nasaba da yaje yajen aikin malamai da tarzomar dalibai ba kakkautawa, saboda haka yai kira ga dukkan masu hannu a sha’anin ilimi, su dubi wannan matsala da idon basira don ganin an farfado da harkokin ilimi a kasar.

A saurari rahoton Souley Barma da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:42 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG