Emmerson Mnangagwa ya lashe zaben shugaban kasar Zimbabwe, a zabenda aka fuskanci tarzoma da zargin mgudi.
Hukumar zaben kasar ta ce Mnangagwa ya samu kashi 50.8 cikin 100 na adadin kuri’un da aka kada, inda ya bai wa abokin hamayyarsa Nelson Chamisa ‘yar tazara a yawan kuri’u.
Chamisa ya kira sakamakon zabe a zaman "kariya" kuma yayi alwashin zai kalubalanci sakamakon zaben a kotu.
Kamin a bayyana sakamakon zaben baki dayansa da misalin karfe daya na daren jumma'a, wani kakakin 'yan hamayya ya bayyana gaban na'urorin daukar magana dana talabijin, inda yayi tur da sakamakon zaben,yace jam'iyyar su bata tantance sahihancinsa ba.
Aka yi cha akansa kamin jami'an tsaro suka awon gaba dashi.
Hukumar har zaben kasar ta ce, mutane da dama sun fita kada kuri’unsu a mafi aksarin lardunan kasar, sannan an samu kuri’u da dama da aka soke sanadiyar rashin ingancinsu.
Baya ga haka, hukumar ta bayyana zaben a matsayin wanda aka samu gagarumar nasara wajen gudanar da shi.
Amma dai ta nuna rashin jin dadinta bisa arangamar da aka samu tsakanin masu zanga zanga da ‘yan sanda, wacce ta yi sanadin mutuwar mutum shida a Harare, babban birnin kasar ta Zimbabwe.
Facebook Forum