Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Ta Kara Taimako Ga 'Yan Gudun Hijira A Habasha


UNHCR
UNHCR

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya tana kara himma ga ayyukan da take yi na taimakon rayukan kusan mutane miliyon guda da rikicin kudu maso yammacin Habasha ya rabasu da muhallansu, kana ta yi kira da a gaggauta aiwatar da shirin sulhu domin kawo karshen tankiya a yankin.

Mai Magana da yawun hukumar 'yan gudun hijiran Andrej Mahecic, yace arcewa daga matsugunai da ya yi kamari a cikin watannin Yuni da Yuli, ya biyo bayan rikicin nan ne da ya bazu a yankin da kuma mummunar cin zarafi bil adama da kungiyoyin yan bindiga suke yi. Yace lamarin ya shafi kwakwalwar mata da yara da suka shedi rikicin.

Yace wadanda suka arcen, sun kwatanta a binda suka gani da mummunar tashin hankali yayin da aka kai hare hare a kauyen, lamarin da ya haddasa kashe kashe da fyade da kashe dabbobi da kuma kona gidaje kurmus. Yace galibin wadanda suka arce basu tsira komai ba sai rayukansu, iyalai sun rabu da juna kana cunkoson mutane a sansanin yan gudun hijiran na yin babbar barazana ga rayuwarsu.

Mahecic ya fadawa Muryar Amurka cewa hukumar yan gudun hijiran ta Majalisar Dinkin Duniya ta tura rukunin masu kai daukin gaggawa a wurin domin kimanta hali da ake ciki, kana sun kara himma wurin raba kayayyakin taimako ga wadanda suka rasa mastugunansu. Ya kara jaddada muhimmancin aikin taimakon da kuma shirin sulhu da gwamnati ke jagoranta.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG