Taron wanda aka gudanar a dakin taro na Afri Hotel da ke Abuja ya samu halartan mata da maza daga kafafen yada labaru daban daban da ma wasu bangarori da dama.
Sunan zauren shine ‘Arewa Women In New Media’ wato Matan Arewa A Kafafen Jarida Na Zamani, kuma aiyukansu zai karade kafafen yada labaru na zamani da a yanzu suke yayi wajen yada labaru cikin sauri.
Wacce ta shirya taron, kuma shugabar ROTV24, Rashida Yahaya Noro, ta ce hakika mata, musamman yan jarida, na fuskantar kalubale a aikin su amma duk da haka suna iya bakin kokarin su wajen yin aiki bisa bin dokoki da kuma karfafa gaskiya da kare al’adu.
Daya da ga cikin mahalarta taron, Hajiya Amina Ibrahim Yusuf, kuma shugabar kamfanin Dija Travel Tours, ta yaba wa taron ta kuma yi kira ga mata da su fito wajen yada kyawawan manufofi tare da yin kira ga gwamnati da dukkan masu ruwa da tsaki da su cigaba da tallafa wa mata.
Zauren ya bukaci jama’ar arewa da su rika mara wa mata baya da basu shawarwari don kare hakkokin yankin mai yawan kabilu a fadin kasa.
Saurari rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5