Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yar Jaridar Da Ta Yi Batan Dabo A Nijar Ta Bayyana


Samira Sabou, ‘yar jarida kuma shugabar kungiyar masu fafutika ta yanar gizo a Nijar
Samira Sabou, ‘yar jarida kuma shugabar kungiyar masu fafutika ta yanar gizo a Nijar

A jamhuriyar Nijer ‘Yar jaridar nan mai fafutuka ta yanar gizo, Samira Sabou da ta yi batan dabo a karshen watan Satumba ta bayyana a ranar Asabar din da ta gabata.

Makusantan Malama Samira sun shafe mako daya cikin zullumi sakamakon rashin sanin inda aka shiga da ita, ballantana a san halin da ta ke ciki.

Lamarin ya auku ne a yammacin Assabar 30 ga watan Satumban 2023, sa'adda wasu mutane sanye da kayan farar hula suka afka gidan Samira Sabou, inda suka yi awon gaba da ita ba tare da sanin takamemen wurin da suka nufa da ita ba.

Haka kuma yunkurin da makusantanta suka yi a ranakun farkon faruwar abin ba don gano inda take bai yi nasara ba.

Hankali ya kara tashi bayan da ‘yan sandan farin kaya suka sanar cewa ba su suka cafke ‘yan jaridar ba.

Kwatsam sai kuma aka ji labarin cewa an gabatar da ita a ofishin ‘yan sandan PJ a karshen mako, abin da ya sa danginta suka garzaya domin duba halin da ta ke ciki.

Abdoulkader Nouhou shine mijin Samira Sabou. Ya ce dole ne hankali ya tashi saboda ba wanda ya san inda ta ke ko halin da ke ciki.

Kawo yanzu ba'a san zahirin dalilin kama wannan mata ba ballantana a san abubuwan da ake zargin ta aikata.

Kungiyoyin kare hakiin ‘yan jarida a nan cikin gida sun bayyana damuwa matuka dangane da abin da ya faru da ‘yar jarida Samira Sabou, ganin yadda lamarin ya wakana cikin wani yanayin da ya saba wa doka.

Kasancewar an sami tabbacin ta na hannun hukumomi a yanzu, ana iya cewa hankali ya dan kwant,a kamar yadda Souleymane Oumarou Brah, sakataren watsa labaran gamayyar kungiyoyin kare hakkin ‘yan jarida ta kasa Maison de La Presse ya bayyana.

Tun a washe garin bacewar ‘yar jarida Samira Sabou bugo da kari shugabar kungiyar ABCA ta masu fafutuka ta yanar gizo, kungiyoyin kasa-da-kasa RSF da Amnesty International suka shiga bin diddigi don ganin cewa ba'a ci zarafinta ba, sakamakon lura da yadda a baya ta ruwaito a shafinta na facebook cewa wasu mutane na yi mata barazana saboda labaran da ta ke wallafawa ko kuma sukar da ta ke yi akan wasu abubuwan da take ganin sun saba wa doka.

Kawo yanzu ba wani bayani a hukunce game da kama wannan mata. Sai dai kungiyar kare hakkin ‘yan jarida ta RSF ta bukaci a gaggauta sakinta ta koma kan aiki ba tare da wani sharadi ba.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG