Samira wace ke shugabancin kungiyar ABCA ta masu fafutuka a yanar gizo ta yi batan dabo a karshen watan Satumba bayan da wasu mutanen da ba'a san ko su waye ba suka saceta a gidanta da ke birnin Yamai, kuma aka rasa inda suka nufa da ita kafin a kai ta ofishin ‘yan sandan farin kaya a ranar asabar din da ta gabata.
A jiya laraba 11 ga watan Okotoba ne aka dauki Samira Sabou daga ofishin ‘yan sandan farin kaya don gabatar da ita a gaban alkali mai bincike, wanda ya saurari ‘yar jaridar da hukumomi suka cafke a ranar Asabar din da ta gabata.
A karshe an yi mata sakin talala, abin da ke nufin za ta iya ci gaba da gudanar da harakokinta amma kuma ta kasance cikin shirin amsa sammaci a nan gaba idan watakila alkali ya bukaci ta yi bayani.
Matakin kotun abu ne da mijinta Abdoulaker Nouhou y ace sun karba da hannu biyu.
Gamayyar kungiyoyin ‘yan jarida ta kasa wato maison de la Presse ta yi na’am da sakin Samira Sabou.
Kafin ta bayyana a ofishin ‘yan sandan farin kaya, an dauki mako guda cur ba tare da sanin takamaimen wurin da ake tsare da Madame Samira ba, wacce wasu mutane sanye da kayan farar hula suka kutsa gidanta suka kuma yi awon gaba da ita cikin wani yanayi mai daure kai.
Wasu na kallon lamarin tamkar wani yunkuri ne na rufe bakin wannan mata jagorar kungiyar masu fafutika ta yanar gizo. To sai dai wani mataimakinta Mamoudou Djibo Hamani na cewa aikin fadakar da jama’a yanzu aka fara.
Yace "muna nan kan bakanmu na ci gaba da aikin sa ido da waye kai da kare hakkin bil adama domin abu ne na sa kai da muke kaunar yinsa. Saboda haka za mu ci gaba da aiki kamar yadda aka saba. Shugabarmu mutun ce jajirtacciya duk irin halin da ta tsinci kanta ba abin da ke katse mata hamzarin aiki. Wannan bai dakatar da ayyukanmu ba hasalima abu ne da ke kara mana kwarin guiwa."
Kawo yanzu ba'a bayyanawa jama’a ainahin abubuwan da ake zargin ‘yan jaridar da aikatawa ba haka kuma lauyanta Maitre Salim da muka kira bai daga wayarsa ba.
Samira Sabou ta yi fice wajen wallafa labarai masu zafi a shafinta na facebook abinda a kwanakin baya ya janyo mata cin fuska daga wasu masu amfani da kafafen sada zumunta, wasun ma har da kalamai irin na barazanar kisan kai saboda a cewarsu, ba ta kishin kasa.
Wasu kuma wasu suna zarginta da kasancewa mai alaka da kasar Faransa kamar yadda ta sanar a shafinta.
Saurari rahoton :
Dandalin Mu Tattauna