ABUJA, NIGERIA - Mahalarta taron sun hada da mata ‘yan takara daga jam’iyyu daban-daban, ‘yan gwagwarmaya, ‘yan jarida, jami’a a hukumar zaben Najeriya INEC, da sauran su.
Taron wanda babbar Edita a Sashen Hausa na muryar Amurya Grace Alheri Abdu ta jagoranta ta ce makasudin shirya taron shine don a bawa mata damar tattauna muhimman batuwa da matsalolin da suke fuskanta a tsakanin su da suka shafi siyasa dama lamuran yau da kullum don zama tsinstinya madaurinki daya.
Yar takarar gwamna a jihar Niger karkashin inuwar jam’iyyar APGA Khadijah Abdullahi Iya ta ce tana fuskantar kalubale da dama a harkar siyasa a matsayin ta na kallabi a tsakanin rawwuna.
Itama ‘yar takarar sanata a Babban birnin Tarayya a jam’iyyar Labour Ireti Heebbah Kingibe wacce ta sha tsayawa takara amma bata yi nasara ba tace wannan karon akwai alamun nasara.
‘Yar gwagwarmaya Zainab Ahmad wacce akafi sani da Bint Hijazi ta ce al’ada da addini na daga cikin abubuwan da yasa mata basa taimakawa mata ‘yan uwansu musamman a harkar siyasa.
A nata bangaren jami’a a sashen yada labarai na hukumar zabe ta kasa INEC Zainab Aminu Abubakar ta karfafawa mata gwiwa dasu fito su kada kuri’arsu don kar a barsu a baya.
Sauran mahalarta taron sun samu damar tofa albarkacin bakin su da kuma bada gudummawa kan abubuwan da suke ganin zasu kawo cigaba a tsakanin mata a Najeriya.
Saurari cikakken rahoto daga Hauwa Umar: