A ranar Lahadi, mataimakiyar shugaban kasar Amurka, Kamala Harris, ta bukaci a amince da kudurin yarjejeniyar tsagaita wuta ta tsawon makonni shida a yakin Isra'ila da Hamas, yayin da ta caccaki Isra'ila kan kin ba da damar kai isassun kayan agaji a Gaza.
“Idan aka yi la’akari da irin wahalhalun da ake fuskanta a Gaza, dole ne a tsagaita bude wuta ba tare da bata lokaci ba akalla tsawon makonni shida masu zuwa, abin da ake kan tattaunawa kenan,” in ji Harris a yayin wani jawabi a birnin Selma da ke jihar Alabama.
A ranar Asabar wani babban jami'in Amurka ya fadi cewa Isra'ila ta amince da yarjejeniyar da aka cimma, wadda a karkashinta za’a tsagaita wuta tsawon makonni shida, idan kungiyar Hamas ta amince ta saki mutanen da suka fi rauni a cikin wadanda ta yi garkuwa da su.
"Wannan zai sa a saki mutanen da aka yi garkuwa da su, a dayan gefen kuma a kai kayan agaji masu yawa," a cewar Harris, inda ta yi kira ga Hamas da ta amince da yarjejeniyar.
"Hamas ta yi ikirarin cewa tana so a tsagaita wuta. To, akwai yarjejeniyar da ake tattaunawa a yanzu. Kuma kamar yadda muka fada, ya kamata Hamas ta amince da wannan yarjejeniyar."
Da kakkausan lafazi kuma ta caccaki Isra'ila, inda ta yi kira ga gwamnatin Firai Minista Benjamin Netanyahu da ta dauki matakin kara kai agaji a Gaza.
"Ya zama wajibi gwamnatin Isra'ila ta kara daukar matakai wajen bari a kai karin tallafin jin kai. Ba tare da bada wata hujja ba," in ji Harris.
Ta kara da cewa "dole ne Isra'ila ta bude sabbin hanyoyin kan iyakoki" kuma "ba tare da sanya wani takunkumi a kan jigilar kayan agaji ba.”
Harin da kungiyar Hamas ta kai ranar 7 ga watan Oktoba ya yi sanadin mutuwar mutane kusan 1,160 a Isra'ila, yawancinsu fararen hula, a cewar alkaluman da kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar bisa ga adadin da hukumomin Isra'ila suka ba da, yayin da ake kyautata zaton an yi garkuwa da mutane kusan 250.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce har yanzu mutane 130 da aka yi garkuwa da su na tsare a Gaza, inda ake kyautata zato 31 daga cikinsu sun mutu.
Martanin hare-haren da sojojin Isra'ila suka mayar ya yi sanadin mutuwar mutane 30,410, yawancinsu mata da yara, a cewar ma'aikatar lafiyar Hamas.