Shugaba Joe Biden ya ce jami'an Amurka suna duba bayanan bangaren biyu game da yadda harin ya faru.
Mai magana da yawun fadar White House Olivia Dalton ta kira adadin wadanda suka mutu a matsayin " mai girman gaske" kuma abun matukar damuwa ne.
"Wannan sabon harin na bukatar a bincika sosai," in ji ta. "Lamarin ya jaddada bukatar fadada ayyukan jinkai don su samu shiga Gaza."
Da farko dai jami'an asibitin Gaza sun bada rahoton wani hari da Isra'ila ta kai kan mutanen da ke zagayen al-Nabusi da ke yammacin birnin.
Shaidu daga baya sun ce sojojin Isra'ila sun bude wuta yayin da mutane su ke zakulo fulawa da kayan abincin na gwangwani daga cikin manyan motoci.
Jami'an Isra'ila sun amince da cewa sojojin sun bude wuta, suna masu cewa sun yi hakan ne saboda a zatonsu mutanen da ke garzayawa zuwa motocin agaji suna da barazana.
Da farko dai sojojin sun ce an kashe mutane da dama wasu kuma sun jikkata sakamakon ture-ture da tattakewa da manyan motoci suka yi musu.
Ofishin firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi irin wannan bayani, yana mai cewa da yawa daga cikin wadanda suka mutu, manyan motocin ne suka murkushe su, bayan da motocin agaji suka cika da mutanen da ke kokarin kwashewa.
"Abubuwa biyu sun bayyan daga hotunan da aka dauka daga jiragen sama," in ji mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka Matthew Miller. " Idan ku ka duba lamarin, za ku ga cewa lamarin ya yi matukar muni, cewa mutane na yin tururuwa ga wadannan motoci saboda yunwa, saboda suna bukatar abinci, saboda suna bukatar magunguna da sauran taimako. Kuma hakan yana nuna maka cewa muna bukatar mu kara himma wajen kai agajin jin kai."
Ma'aikatar lafiya ta Gaza ta Hamas ta ce sanadiyar lamarin na ranar Alhamis, yanzu adadin wadanda suka mutu ya haura 30,000 a yakin da Isra'ila ta kwashe kusan watanni biyar tana yi da mayakan Hamas wanda aka fara a ranar 7 ga watan Oktoba tare da wani harin ba-zata da Hamas ta kai Isra'ila wanda ya kashe mutane 1,200.
Majalisar Dinkin Duniya ta fada jiya Laraba cewa, ma’aikatan agaji da ke kokarin raba ko karbar kayan agaji a zirin Gaza na fuskantar kalubalen da ke barazana ga rayuwa.
Dandalin Mu Tattauna