A yini na biyu na zanga-zangar neman a kawo karshen tsadar rayuwa a Najeriyar musamman daga bukataun da masu zangar-zangar suka gabatar na a dawo da tallafin man fetur da aka janye, a kawo karshen matsalolin tsaro a arewacin Najeriya, a rage albashin masu rike da mukamman siyasa, jami’an tsaro sun kara tarwatsa wadanda suka fito a unguwar Berger da tiya gas inda suka koma filin wasan M.K.O Abiola daga bisani kuma suka doshi dandalin Eagle square.
Abin mamaki a fitowar masu zanga-zangar na yau shi ne yadda wata mata mai dauke da jaririyar da aka harba wa hayaki mai sa kwalla a rana ta farko Suwaiba Abdullahi ta sake fitowa, tana mai cewa suna nan daram kan manufofin da ya fito da su musamman tabbatar da cewa an dawo da tallafin man fetur, kawo sauki a hauhawar farashin kayan abinci da dai sauransu.
Matashi Kamilu Rabiu Danlami ya tofa albarkacin bakin shi a kan tsadar rayuwa yana mai cewa babu wanda zai samar musu abubuwan da suke nema idan ba gwamnati ba.
Shi ma 'dan gwagwarmayya, kuma lauya mai kare hakkin 'dan adam, Deji Adeyanju, ya bayyana yadda jami’an tsaro suka kara afka musu, inda ya ce mutane zasu ci gaba da fitowa zanga-zanga muddin gwamnati ta ci gaba da nuna halin ko in kula ga yanayin da ‘yan kasa ke ciki na matsi.
A kokarin mu na neman ji ta bakin gwamnatin tarayya a yau, wayoyin tarhon masu magana da yawun ta, ba sa shiga kuma ba su ce uffan ba a kafoffin su na sada zumunta da suka saba wallafa sakonni kan matsayin gwamnati na yau da kullum.
Masu zanga-zangar dai na ci gaba da gudanar da zanga-zanga a Abuja, Legas, Ribas, Kano da wasu garuruwa da dama domin mika korafe-korafensu kan sauye-sauyen tattalin arzikin da ya yi sanadiyar tashin farashin kayayyakin masarufi da kuma kara jawo wa talakawan Najeriya wahala inda masana ke cewa kamata ya yi gwamnatin tarayyar ta fito da yi jawabi da su.
Saurari cikakken rahoto daga Halima Abdulrauf:
Your browser doesn’t support HTML5