Wata kungiyar kare hakkin bil adama ce a yau Juma’a ta bayyana haka yayin da kuma da hukumomi suka ce an kashe ‘dan sanda tare da jikkata wasu da dama sakamakon zanga-zangar tsadar rayuwa a fadin kasar.
Hukumomi kuma sun ce an kashe wasu masu zanga-zanga hudu tare da raunata 34 a wani harin bam a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar, inda yaki mafi dadewa a duniya da ‘yan ta da kayar baya ya yi sanadin ficewar miliyoyin mutane daga gidajensu ya kuma haifar da matsalar yunwa.
‘Yan sandan Najeriya sun ce sama da masu zanga-zanga 300 ne aka kama tare da sanya dokar hana fita a wasu jihohi hudu na arewacin kasar bayan sace dukiyar gwamnati da ta jama’a.
Shugaban ‘yan sanda na kasa, Kayode Egbetokun, ya bayyana a daren Alhamis cewa, ‘yan sandan na cikin shirin ko-ta-kwana kuma suna iya neman taimakon sojoji.
Daraktan Amnesty International a Najeriya Isa Sanusi ya ce a wata hira da kungiyar ta yi da kanta ta tabbatar da mutuwar wadanda shedu, da iyalan wadanda abin ya shafa, da lauyoyi suka ruwaito.
An dai gudanar da zanga-zangar ne saboda karancin abinci da kuma zargin gwamnati da cin hanci da rashawa a kasar da ta fi kowacce yawan al'umma a Afirka.
Jami’an gwamnatin Najeriya na daga cikin wadanda suka fi samun albashi a nahiyar Afirka, sabanin cewa kasar na da matalauta da yunwa duk da kasancewarta daya daga cikin manyan masu arzikin man fetur a nahiyar.
-AP
Dandalin Mu Tattauna