BAUCHI, NIGERIA -Wadansu mutane guda hudu da ake zargin masu tonon ma’adinai ta barauniyar hanya ne sun rasa rayukansu a jihar Bauchi, a cikin ramin da suke tonon ma’adinan.
Akan kira masu tonan ma’adinai ta barauniyar hanya da sunan "‘yan lamban gudu" a kasuwar hada-hada da kuma tonan ma’adinai.
Wannan hatsari ya faru ne a karamar hukumar Ningi dake jihar Bauchi a kauyen da ake kira Yadagungume na unguwar Kogo a ranar Asabar din da ta gabata.
Bincike na nuni da cewar masu sana’ar lamban gudan, basu da kwarewa kuma basu amfani da na’urar zamani don yin tono, yawancin abubuwan da suke amfani dasu wajen tonon sune diga da cebur da fartanya, wanda wannan hanyar kan jawo illoli wa al’umma dakuma muhalli.
Zaharaddeen Bala Dan Madami, mai sa ido kan harkar tonon ma’adinai a yankin karamar hukumar Ningi, ya ziyarci wurin da hatsarin ya faru, yayi mana karin haske game da abubuwan da ya gane wa idandunaansa.
A halin da ake ciki, gwamnonin jihohin Arewa maso Gabas a taronsu na takwas da suka gudanar a Maiduguri jihar Borno, a wata sanarwa bayan taron sun bukaci gwamnatocin jihohin da su tabbatar da bin dokokin gudanar da harkokin neman ma’adinai kamar yadda dokar yin amfani da filaye ta kasa ta tanada.
Saurari cikakken rahoto daga Muhammad Abdulwahab:
Your browser doesn’t support HTML5