Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Chinar Da Aka Ceto Daga Hanun Yan Bindiga Sun Fara Samun Kulawar Asibiti


Yan Kasar China Da Sojojin Najeriya suka ceto bayan anyi garkuwa da su
Yan Kasar China Da Sojojin Najeriya suka ceto bayan anyi garkuwa da su

Jami’an Najeriya sun fada a ranar Litinin cewa wasu ‘yan kasar China bakwai na sami kulawar likitoci bayan an ceto su daga hannun masu garkuwa da mutane inda suka shafe kusan watanni shida ana garkuwa da su.

Sojojin Najeriya sun kwato mutanen da aka sace ne a wani samame da suka kai karshen mako a jihar Kaduna da ke arewacin kasar.

Kakakin rundunar sojin saman Najeriya, Gabriel Gabkwet ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, inda ya ce an kubutar da ‘yan kasar China ne daga yankin Kanfani Doka da Gwaska da ke jihar Kaduna bayan wani farmaki da suka kai cikin dare.

Ya ce masu garkuwan sun yi watsi da wurin buyansu tare da wadanda suka sace da ma makamansu.

Ya ce an kwashe sama da watanni biyar suna hannun ‘yan ta’addan da suka yi garkuwa da su a wani wurin da ake hakar ma’adinai a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.

Gabkwet dai bai amsa kiran da Muryar Amurka ta yi masa nan take ba.

A wata sanarwa da gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello ya fitar a jiya Litinin, ya yabawa rundunar sojin sama bisa wannan nasarar da suka samu, ya kuma ce hukumomi za su ci gaba da hada kai da dukkan jami’an tsaro a jihar domin tabbatar da ‘yan kasa sun samu sukuni.

Jami’ai sun ce an kai ‘yan kasar China da aka ceto zuwa wani asibitin da ba a bayyana ba.

A harin da aka kai a watan Yuni a wurin hakar ma'adinan, an kashe jami'an tsaro akalla 22 da suka hada da 'yan sanda da sojoji.

A ranar Litinin, kakakin karamar hukuma a yankin Kaura a jihar Kaduna ya shaidawa gidan talabijin na Channels da ke Legas cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe akalla mutane 37 a wani harin da suka kai ranar Lahadi tare da kona gidaje sama da 100.

‘Yan sanda ba su ce uffan ba kan faruwar lamarin amma wani mai sharhi kan harkokin tsaro Chidi Omeje ya dora alhakin tashin hankalin a kan tserewar daruruwan fursunonin da aka yi a gidan yarin Abuja a watan Yuli.

“Lokacin da wannan batun gidan yari ya faru, kuma aka ce mana gomman ‘yan ta’adda da ake tsare da su sun tsere, a ina kuke ganin suka je? Ba a gaya mana cewa an sake kama su ba, don haka yanzu sun je sun sake farfado da ‘yan ta’addan. “

Sama da shekaru 13 ne Najeriya ta kwashe tana yaki da kungiyar Boko Haram da sauran kungiyoyin tada kayar baya a yankin arewa maso gabashin kasar. Kimanin mutane 300,000 ne aka kashe a rikicin.

Hukumomin kasar na kuma kokawa kan yadda za a shawo kan gungun masu satar mutane don neman kudin fansa da ke addabar sauran yankunan kasar.

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG