Masu harin kunar bakin wake sun kashe mutane tamanin a Pakistan

Daya daga cikin mutanen da tagwayen harin kunar bakin wake ya raunana. Ana okarin sa shi a mota domin a kai shi asibiti.

Domin ramuwar gaiyar kashe Osama Bin Laden da Amirka tayi a makon jiya, wasu masu harin kunar bakin wake sun kashe mutane tamanin a kasar Pakistan. Yau juma'a aka kai tagwayen harin.

Masu harin kunar bakin wake, yan kungiyar Taliban reshen Pakistan sun kaiwa wata cibiyar horon sojojin laima a arewa maso yammacin Pakistan hari suka kashe akalla mutane tamanin domin ramuwar gaiyar kashe Osama Bin Laden da Amirka tayi a makon jiya. A yau juma'a tagwayen harin bama baman ya auku a cibiyar Constabulary a gundumar Charsadda na lardin Kyyber Pakhtunkhwa. Jami'ai sunce yawancin wadanan aka kashe sabbin kurata ne. Fiye da mutane dari da ashirin suka ji rauni, wasu sunji mumunar rauni. Shedun gani da ido sunce an kai harin ne a daidai lokacinda kurata ke shiga bas din da zata kai su gida domin su fara hutu. Mai magana da yawun kungiyar Taliban reshen Pakistan yayi ikirarin cewa kungiyarsa ce keda alhakin tagwayen harin kunar bakin waken, kuma ya lashi takobin cewa kungiyar zata kai wasu karin hare hare domin ramuwar kisan da Amirka ta yiwa Osama Bin Laden. Shugabanin Pakistan da ofishin jakadancin Amirka a birnin Islamabad sun yi Allah wadai da harin kunar bakin waken.

Related Video Footage