Shugaban kungiyar al-Qaidar kasashen Larabawan yankin tekun Arebiya ya yiwa Amurka gargadin kawo ma ta karin hare-haren ramuwar gayyar kisan da aka yiwa Osama Bin Laden a kasar Pakistan a makon jiya.
A cikin wata sanarwar da aka buga jiya Laraba a intanet, shugaban kungiyar wanda ke kasar Yemen da zama,Nasir al-Wuhayshi ya gayawa Amurkawa cewa kar su yaudari kan su, su zaci cewa shikenan magana ta kare don an kashe Bin Laden. Ya ce garwashin Jihadi yana na nan giris, kuma abun da ke tafe nan gaba kasaitacce ne mai gawurta kuma zai fi gayya ciwo.
Kungiyar al-Qaidar ta yi wannan gargadi ne a daidai lokacin da dan majalisar dattawan Amurka, John Kerry ya sanar da cewa a makon gobe zai tashi zuwa kasar Pakistan da nufin yin kokarin gyara hulda tsakanin kasashen biyu bayan samamen da sojojin Amurka su ka kai har gidan Osama Bin Laden a birnin Abbottabad a arewacin kasar.
Samamen na ranar biyu ga watan Mayu ya kara lalata hulda tsakanin Amurka da Pakistan .
A jiya Laraba,shugaban kwamitin majalisar wakilan Amurka mai kula da harakokin leken asiri, Mike Rogers ya fada cewa ta yiwu a kasar Pakistan akwai wasu daidaikun mutanen da su ka san da cewa Osama Bin Laden ya na boye a kasar, amma kuma ya ce, har yanzu dai babu alamun da ke nuna cewa manya-manyan jami'an gwamnatin kasar ta Pakistan su na sane kuma sun ba shi mafaka.
Kakakin Fadar Shugaban kasar Amurka, Jay Carney ya ce ana da cikakkiyar hujjar kai harin wanda ya bayar da nasara akan mai sana'ar kisan kan gama gari.
A jiya Laraba Frayim Ministan kasar Pakistan Yousuf Raza Gilani ya gayawa manema labarai cewa bai kamata Pakistan ta sake ana yin amfani da ita ana aikata ta'addanci ba, sannan kuma ya bayar da umarnin gudanar da wani binciken soji game da yadda aka yi Osama Bin Laden ya shiga kasar babu wanda ya sani.
Amma shugaban jam'iyyar hamayyar kasar kuma tsohon Frayim Minista,Nawaz Sharif ya yi fatali da batun gudanar da binciken, sannan ya bukaci da lallai sai dai babban Jojin kasar Pakistan ya jagoranci wani bincike mai zaman kan shi a kan Bin Laden da kuma harin na Amurka wanda ya halaka shi.
Haka kuma Sharif ya soki lamirin hukumar leken asirin kasar Pakistan saboda ta gaza gano samamen na Amurka kafin ta kai shi sannan ya nanata cewa cin mutunci ne ga 'yancin kan kasar Pakistan da martabar ta.
Gilani ya yi watsi da zargin cewa rundunar sojojin kasar Pakistan da hukumar leken asirin kasar sun hada baki ko kuma ba su da katabus don sun kasa gano cewa Bin Laden ya na zaune a cikin kasar. Sannan kuma ya caccaki Amurka saboda harin da ta kai, kuma ya yi jan kunnen cewa daukan irin wannan mataki na yin gaban kai da Amurka ta yi, na iya haifar da wani mummunan sakamako.