Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Barack Obama Yace Alfanun Kamo Bin Laden Shi Ya Sa Ya Amince Da Farmakin Da Ya Kashe Madugun Na Al-Qa'ida

Mr. Obama ya ce duk wanda ya ke ganin abin da ya faru ga shugaban ‘yan ta’adda bai dace ba to ya kamata a binciki kwakwalwarsa.

Shugaban Amurka Barack Obama ya ce ya bayar da umurnin kai hari kan shugaban al-Qa'ida, Osama bin Laden, ne a bayan ya auna ya ga alfanun yiwuwar samin mutumin da ake nema ruwa a jallo ya dara kasadar dake tattare da wannan.

Mr. Obama ya fadi a yayin wata hira da shi da aka yada ta gidan Talabijin din CBS a jiya Lahadi cewa abinda ya fi damunsa ita ce lafiyar sojojin kundumbalar da suka kai farmakin, amman sam bai damu da yiwuwar kashe bin Laden ba. Shugaba Obama ya ce samamen shi ne “minti 40 da ya fi tsawo” a rayuwarsa, im banda lokacin da diyarsa Sasha ta kamu da ciwon sankarau lokacin tana wata uku da haihuwa.

Mr. Obama ya ce duk wanda ya ke ganin abin da ya faru ga shugaban ‘yan ta’adda bai dace ba to ya kamata a binciki kwakwalwarsa.

Ya ce har yanzu ba a tantance ko Pakistan ta san da kasancewar bin Laden a kasarta ba, amma a bayyane yake cewa bin Laden na da masu taimaka masa a Pakistan, da har ya iya zama cikin wani katafaren gida na tsawon shekaru 5 zuwa 6. To amma bai zargi jami’an Pakistan da laifin bayar da mafaka ga dan ta’addar da aka fi nema a duniya ba.

A wata hira jiya Lahadi da gidan talabijin din NBC, wani babban jami’in gwamnatin Amurka yace duk da mutuwar bin Laden, har yanzu akwai barazanar ta’addanci daga al-Ka’ida.

XS
SM
MD
LG