Jirgin Jigilar kayan kimiyya na Amurka Endeavour, a ran litinin ya daga zuwa sararin samaniya daga tashar cibiyar ayyukan kimiyyar sararin samaniya ta Kennedy a jihar Florida, Jirgin jigilar yana dauke da ‘yan sama jannati shida. Biyar Amerkawa da dan Italiya guda. Ana kyautata cewar wannan itace jigila ta kusa da ta karshe kafin ya tafi hutu.
Bayan isar jirgin jigilar sararin samaniya, sai ya rabu da tauraron duniya sannan ya shiga aikinsa na zagaya Falaki. Cibiyar kula da ayyukan binciken sararin samaniya ta Amurka NASA , ta bada sanarwar cewa dukkan injuna da na’urorin binciken jirgin sunan nan kalau, kuma ba wani taraddadin samun wata jikkata a jikin jirgin jigilar. Ana kuma kyautata cewar jirgin jigilar zai isa tashar ayyukan jiragen jigilar kasa da kasa da misalin karfe takwas na safiyar laraba.
Jirgin jigilar kayan kimiyyar na Amurka, na karkashin kulawar dan sama jannati Mark Kelly, wanda aka harbi matrsa Giffords,‘yar majalisar dokokin Amurka da yanzu ake jiyyata a wani Asibitin Amurka. Likitocin dake dubata sun bata iznin zuwa kallon harba kumbon zuwa sararin samaniya.