Rundunar sojojin Pakistan ta mika takardar kuka da babbar murya, a bayan da aka yi musayar wuta a tsakanin sojojinta da jiragen helkwafta na NATO a bakin iyakar Pakistan da Afghanistan.
Pakistan ta ce sojojinta dake wata tashar bakin iyaka sun bude wuta talata da safiya a lokacin da wadannan jiragen saman helkwafta suka kutsa cikin yankin Pakistan. Ta ce sojoji biyu sun ji rauni a musayar wutar da aka yi.
NATO ta tabbatar da cewa akwai wasu helkwaftocinta da suka yi shawagi a yankin bakin iyakar, ta kuma ce tana binciken al’amarin.
Wani jami’in soja na wata kasar yammaci a Kabul yace helkwaftocin su na bangaren Afghanistan na bakin iyaka a lokacin da aka bude musu wuta daga cikin Pakistan. Yace daya daga cikin helkwaftocin ya maida martani, a bayan da aka yi harbi kansa har sau biyu.
Wannan musayar wuta ta jiya talata a kusa da yankin Datta Khel a lardin Waziristan ta Arewa, ta zo a daidai lokacin ad tankiya ta karu a tsakanin Amurka da Pakistan, a bayan farmakin da Amurka ta kai ta kashe shugaban al-Qa’ida, Osama bin Laden, a birnin Abbottabad.