Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pakistan Ta Amince Amurka Tayi Magana Da Matan Bin Laden


Frayin Ministan Pakistan Yusuf Reza Gilani
Frayin Ministan Pakistan Yusuf Reza Gilani

Wani kusar gwamnatin Amurka yace nan bada dadewa ba Pakistan zata baiwa jami’an Amurka iznin suyi wa matan tsohon madugun kungiyar al-Qaida, Osama Bin Laden su ukku tambayoyi. Matan suna tareda Bin Laden lokacinda aka kashe shi a makon jiya.

Wani kusar gwamnatin Amurka yace nan bada dadewa ba Pakistan zata baiwa jami’an Amurka iznin suyi wa matan tsohon madugun kungiyar al-Qaida, Osama Bin Laden su ukku tambayoyi. Matan suna tareda Bin Laden lokacinda aka kashe shi a makon jiya.

Matan suna a hannun hukumomin Pakistan ne tun ran 2 ga watan nan na Mayu, ranarda sojan na Amurka suka kai hari akan gidan na Bin Laden, suka kashe shi. Jami’an Amurka din sunce tambayoyin da zasuyi wa matan, hade da bayanan da suka kwaso daga gidan na Bin Laden, zasu taimaka wajen kara fahimtar aiyukkan kungiyar ta al-Qaida.

Ta wani gefen kuma…Jami’an leken assirai na Pakistan din sunce wani farmaki da wani karamin jirgi maras matuki na Amurka ya kai akan iyakar Pakistan din da Afghanistan, ya hallaka mutane ukku. jami’an sunce rokoki biyu da aka harba sun fada ne akan wata mota dake shigewa ta cikin yankin Waziristan. Sai dai har yanzu su wadanda aka kashen, ba’a tantace ko su wanene ba.

Pakistan dai ta jima tana neman Amurka ta daina kai irin wadanan hare-haren rokoki ta irin wadanan kananan jiragen, abinda tace ya sabawa ‘yancinta na zaman kasa mai cin gashin kanta.

To amma su jami’an Amurka basu taba fitowa fili suka amsa cewa suna kai wadanan hare-hare a cikin Pakistan ba, amma sun sha tabattarwa wasu kafafen watsa labarai maganar cewa akwai jiragen dake kai farmakin.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG