Masu Ababen Hawa Na Kokawa Kan Karin Kudin Rijista Da Lasisin Mota

Lokacin da aka iso da dailban a cikin motoci

Wannan ya biyo ne bayan sanarwar da gwamnatin Najeriya ta fitar a makon da ya gabata, inda ta ce karin na daga cikin matakan samun ci gaba  ta fannin samun kudaden shiga ga kasar.

Masu ababen hawa da suka hada da direbobin motocin kasuwa da na bukatun kansu na kokana kan kari a kudin yin rijista da samun lasisi inda suka bukaci gwamnati ta sake duba hauhawar farashin da aka samu ga talakawa a masu neman lasisin tuki sabbin da tsaffin a duk fafin kasar.

Koke-koken ya biyo bayan sanarwar da gwamnatin tarayyar Najeriya ta fitar a makon da ya gabata, inda ta ce karin na daga cikin matakan samun ci gaba ta fannin samun kudaden shiga ga kasar don aiwatar da ayukan da za su amfani 'yan kasa.

Saidai akasarin mutane a birnin tarayya Abuja da ma wasu jihohi a fadin kasar suna kokawa kan matakin tare da yin kira ga gwamnati da ta yi watsi da dalilan da kwamitin hadin gwiwa wato JTB da gwamnatin ta kafa ya gabatar wanda ya dauki wannan matakin.

Akasarin direbobin kasuwa sun ce bai kamata a yi karin ba saboda ana dora musu harajin da ya fi karfin kudadden shigar da su ke samu.

Haka kuma sun ce matakin na zuwa ne a daidai lokacin da yan kasa ke fuskantar tsadar rayuwa bisa yanayin matsin tattalin arziki da ya kai ga kayayyakin masarufi suka yi tashin gwauron zabi.

Wasu ‘yan Najeriya dai sun ce akwai bukatar shugaba Muhammadu Buhari ya shiga tsakani a madadin talakawa, ta hanyar kira ga hukumomin samar da kudaden shiga da su rika kamanta adalci ga talakawa.

Idan ana iya tunawa, a cikin makon jiya ne kwamitin hadin gwiwar gwamnati ya sanar da cewa daga ranar 1 ga Agusta da muke ciki, kudin samun takardun masu ababen hawa na kansu da kuma na motocin kasuwa da dai sauransu, zai koma Naira 18,750, sabanin Naira 12,000 da ake biya a da.

Haka kuma, kwamitin ya amince da cewa a rika cajar Naira 10,350 da kuma Naira 15,450, sabanin Naira dubu 6,450, da kuma Naira dubu 10,450 a lasisin direbobi na tsawon shekaru uku da na shekaru biyar daga yanzu.

Kwamitin JTB ya kuma umarci dukkan hukumomin jiha dake kula da aikin samun kudaden shiga na cikin gida da su tabbatar da aiwatar da tsarin ta hanyar bin diddigin biyan sabbin kudaden da aka amince da su na rijista da samun lasisi.

Kwamitin JTB wanda gwamnati ta kafa a karkashin tanadin doka sashe na 86 sakin sashe na 1 na PITA a shekarar 2004, shi ne kwamiti mai cikakken iko kan hukumomin karbar haraji a Najeriya.

Mahukunta a hukomin karbar haraji a jihohin Najeriya sun tabbatar da samun wasikar kwamitin JTB kan aiwatar da sabon farashin samun takardun mota inda direbobi suka yi ta bayyana rashin jin dadin su kan matakin kwamitin tare da neman shugaba Buhari ya sauya shi don saukakawa talakawa rayuwa a wannan lokaci na matsin tattalin arziki,