Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Za Ta Shiga Kungiyar Harkokin Kasuwancin Afirka


Kasuwanci a daya daga cikin kasuwannin Lagos
Kasuwanci a daya daga cikin kasuwannin Lagos

Bayan an yi taruka da bitocin fadakarwa a duk fadin Najeriya da ‘yan kasuwa da masana akan harkokin kasuwanci, yanzu Najeriya ta shirya ta shiga kungiyar harkokin kasuwancin Afirka da babu tsangwama a ciki.

A taron bita da kuma wayar da kawunan masana harkokin kasuwanci da ‘yan kasuwa da ofishin cibiyar kula da harkokin kasuwanci na Najeriya ya shirya a Lagos ma jihohin kudu maso yammacin kasar guda shida an bayyana cewa Najeriya zata ci moriyar kasuwar.

Babban daraktan cibiyar Ambassador Chidu Osakwe ya bayyana irin alfanun da Najeriya zata samu sanadiyar kasancewarta cikin kungiyar harkokin kasuwanci ta Afirka. Ya yaba da matakin da shugaba Muhammad Buhari ya dauka na kin sa hannu a yarjejeniyar kafa kungiyar harkokin kasuwancin har sai da ya samu amincewar ‘yan kasuwar kasar tare da na masana harkokin kasuwanci.

Ambassador Osakwe yace idan Najeriya ta shiga kasuwar ta Afirka babu shakka tattalin arzikinta zai fi na kasar Australia girma. Hakan zai tabbata ne idan Najeriya ta taka rawar da ta kamata a kasuwar Afirkan.

A yanzu alkalumma sun nuna kasashen Afirka na kasuwanci tsakaninsu da ya kai na dalar Amurka biliyan daya da miliyan dari biyu kowace shekara. Amma da zara an fara kasuwar, kasuwanci zai habaka fiye da kashi hamsin daga cikin dari. Ambassador Osakwe, yace wannan gajiya ce da kasashen Afirkan zasu samu. Misali, Najeriya zata ci gajiyar fitar da kayayyakin da ake kerawa a kasar zuwa wasu kasashen Afirka. Tun kafin ma wannan sabuwar yarjejeniyar Najeriya ke fitar da kaya zuwa wasu kasashen makwafta har zuwa kasar Congo.

Injiniya Awal Ibrahim, daya daga cikin shugabanin masu kananan masana’antu, ya ce sun amince Najeriya ta shiga kungiyar kuma ya kamata gwamnati ta tashi ta yi wasu gyare-gyaren da zasu ba kasar damar rike matsayinta na kasancewa mai babban tattalin arziki a nahiyar. Yana gudun kada wasu kananan kasashe su hada baki da kasashen waje suna sarafa masu kayayyaki da sunan cikin kasashensu aka sarafasu.

Mulifat Sani shugabar kamfanin hada motocin Mulifat Motors ta ce sun amince Najeriya ta shiga kungiyar. Najeriya tana da duk abun da take bukata na ci gaba saboda ana sarafa wasu kayayyaki da ake fitar dasu zuwa wasu kasashe da can, amma yanzu babu su.

A saurari karin bayani a rahoton Babangida Jibrin

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:45 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG