Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

TARABA: Karon Motocin Dake Dauke Da Man Fetur A Garin Zing Ya Hallaka Mutane Da Dukiyoyi


Motocin tanka dauke da man fetur da suka kama wuta
Motocin tanka dauke da man fetur da suka kama wuta

Rahotanni daga jihar Taraba arewa maso gabashi Najeriya ,na cewa mutane da dama ne suka rasa rayukansu sakamakon wani mummunar hatsarin tankokin man fetur da ya auku a garin Zing.

Rahotanni dai na cewa wasu tankokin man fetur guda biyu ne suka kama da wuta a garin na Zing,sakamakon matsalar rashin birki,lamarin da ya jawo asarar rayuka da dama baya ga kona motoci,Babura da kuma shagunan dake bakin hanya.

Kuma hatsarin ya faru ne yayin da ake cikin ganiyar cin kasuwar garin,kamar yadda wasu shaidun gani da ido suka tabbatar.

Al’umman gari dai sun yi kokarin kashe wutar to amma hakarsu bata cimma ruwa ba,kasancewar babu yan kwana kwana ko kuma motar kashe gobara a cewar wani mutum, wanda ya tsallake rijiya da baya.

To sai dai kuma yayin da ake hada hancin alkalumman wadannda lamarin ya rutsa da su,kakakin rundunan yan sandan jihar ya tabbatar da mutuwar mutane takwas baicin wadanda aka garzaya dasu asibiti.

Kakakin y ace birkin motar tankar man fetur dake tafiya ne ya tsinke lamarin da ya sa ta buga wata mota da ita ma tana dauke da man fetur dake gefen hanya a tsaye. Nan take gobara ta tashi inda akwai cunkoson mutane dake hada hadar kasuwanci a kasuwa. Nan wutar da ta tashi ta kone mutane da motoci da shaguna.

‘Yan sanda na ci gaba da tattara bayanai da kuma sanin adadin wadanda suka rasa rayukansu da kuma suka jikata.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG