Baicin biranen Enugu da Aba galibin al’ummar kudu maso gabashin Nigeria sun fita sun ci gaba harkokinsu na yau da kullum. Sun yi kunnen kashi ga umarnin kungiyar ‘yan rajin kafa kasar Biafra, wato IPOB.
Tun can baya dai kungiyar ta ayyana ranar 30 ga watan Mayu a matsayin ranar da al’ummar kudu maso gabas zasu zauna gidajensu, babu shiga ,babu fita, ayyuka kuma su tsaya cik.
To sai dai hakan kungiyar bai cimma ruwa ba. Alhaji Maigari Bello wani dan kasuwa kuma mazaunin Awka babban Birnin jihar Anambra ya ce komi yana tafiya daidai. Babu wata matsala a garin saboda babu wanda ya zauna gida. Kowa na ci gaba da harkarsa. Yace suna ci gaba da gudanar da harkokin kasuwancinsu.
Haka ma lamarin yake a Birnin Abakaliki babban Birnin jihar Ebonyi inda Malam Baballa Muhammad Gamarya ya bayyana cewa suna ci gaba da harkokinsu, babu wani abu. Makarantu ma na bude. Babu wanda ya bi umurnin IPOB. Gwamnan jihar ma ya sha alwashin ladabtar da duk wanda ya bi umurnin.
Mr. Emmanuel Nnanna, wani mazaunin Umuahia a jihar Abia, yace babu abun da ya faru a garin. Suna zaman lafiya. Mutane sun fito, ma’aikatan gwamnati sun fita aiki, makarantu sun bude kasuwanni kuma sun ci gaba da hada hada.
Amma a Birnin Aba, babban Birnin jihar Abian Malam Usman Shehu ya ce babu wanda ya fito. Shaguna suna rufe, babu zirga zirgan motoci, haka ma kasuwanni suma suna rufe.
A Enugu ma babban Birnin jihar Enugu bada canja zani ba, domin komi ya tsaya cik. Babu aiki, babu makarantu babu kasuwanni balantana motocin haya. Mr. Chinedu Ugochukwu ya ce yana ganin an bi umurnin a Enugu saboda ‘yan kasuwa sun rufe shagunansu. Amma bankuna sun bude
Saurari karin bayani a rahoton da Alphonsus Okoroigwe ya aiko
Facebook Forum