Martanin Kasashen Kungiyar AES Bayan Da ECOWAS Ta Sake Gayyatarsu

Lokacin taron Kungiyar AES na farko a Yamai, 6 Yuli, 2024

‘Yan Nijar sun fara mai da martani bayan da kungiyar CEDEAO ta jaddada aniyar ci gaba da tuntubar kasashen Burkina Faso, Mali da Nijar don ganin sun sake komawa sahun mambobinta.

Kasashen sun dai sanar da cewa sun fice daga kungiyar ta raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrikar ne a watan Janairun da ya gabata sakamakon zarginta da kasancewa ‘yar amshin shatan Faransa.

Watanni kusan bakwai bayan ficewar kasashen AES daga ECOWAS har yanzu shugabanin kasashen kungiyar ta yankin Afrika ta yamma na ganin bukatar maido da wadanan kasashe a sahun dangi.

Shugaban kasar Senegal Bassirou Diomaye Faye ne aka dora wa nauyi amma kuma zai iya hada guiwa da Faure Eyadema na Togo, abin da masanin sha’anin diflomasiya Moustapha Abdoulaye ya ce ya na da kyaukyawan zato kan tasirin bin hanyar laluba a wannan dambarwa.

Sai dai har yanzu wasu ‘yan Nijar na cewa ba su manta ba da barazanar harin da CEDEAO da ta ayyana a washegarin juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023. Saidou Abdoul Nasser na daga cikin masu kallon kungiyar da abinda suke kira babban tabo.

Jigo a kungiyar AEC Kaka Touda Goni Mamadou na cewa ya kamata jama’a ta yi la’akari da girman alakar da ke tsakanin Burkina Faso, Mali da Nijar da a dai gefe sauran makwafta.

A jajibirin taron ECOWAS na Abuja, kasashen AES a na su bangare sun gudanar da taron koli na farko a nan Yamai inda shugabanin gwamnatocin mulkin sojan uku suka rattaba hannu kan takardun jaddada hadin kai a tsakaninsu a matsayin hadakar Confederation AES, abinda ke nufin tafiya ta kama hanya.

A wata bidiyon da ta karade kafafen sada zumunta a karshen taron na jiya Lahadi shugaban hukumar gudanarwar CEDEAO Oumar Toure ya yi tunatarwa akan cewar ficewar Burkina Faso, Mali da Nijar na iya haddasa cikas wa kai da kawon jama’a domin tabbatuwar wannan kudiri na iya sanadin shimfida tsarin takardar bisa kafin ‘yayan kasashen uku su sami izinin shiga kasashen kungiyar ta raya tattalin arzikin yammacin Afrika yayinda a nan Nijar wasu ke ganin hana wa wadancan kasashe ratsa sararin samaniya na iya zama kwakwaran martani.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Martanin Kasashen Kungiyar AES Bayan Da ECOWAS Ta Sake Gayyatarsu.MP3