Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Mulkin Sojin Nijar Ya Ce Ficewarsu Daga ECOWAS Tabbatacciya Ce


Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar
Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar

NIAMEY, NIGER - Janar Abdourahamane Tiani da ke bayani a kafar talabijan mallakar gwamnatin kasar Nijar ya bayyana cewa kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso sun kaddamar da yunkurin samar da takardun kudi na kashin kansu da nufin katse igiyar da Faransa ke amfani da ita don ci gaba da mulkin mallaka, saboda haka lokaci na nan tafe da zasu fice daga kungiyar UEMOA.

Ibrahim Traore - Burkina Faso – Abdourahamane Tiani - Niger – Assimi Goïta - Mali
Ibrahim Traore - Burkina Faso – Abdourahamane Tiani - Niger – Assimi Goïta - Mali

Janar Abdourahamane Tiani a hirarsa ta sama da awa guda da ‘yan jaridar kafafen gwamnatin Nijar ya dauki lokaci mai tsawo ya na tarihin kafuwar CEDEAO da ainahin makasudin kafata kafin ya kai ga fayyace dalilan da ya sa Nijar hada kai da Burkina Faso da Mali don ficewa daga sahun mambobin kungiyar.

Ya na mai dora alhakin dambarwar da ke tsakanin kasashen uku da a wani gefe kan ECOWAS da kuma wuyan wasu shugabanin da ya kira ‘yan amshin shatan Faransa.

Shugaban majalissar CNSP ya jaddada cewa bakin alkalami ya bushe game da ficewar kasashen AES daga ECOWAS.

Mali Niger Burkina Faso ECOWAS
Mali Niger Burkina Faso ECOWAS

Ya na mai zargin Faransa da shirya wata makarkashiya da zummar haddasa fitina a Nijar.

Shugaban gwamnatin mulkin sojan ya sanar cewa akwai yiwuwar Nijar da Mali da Burkina Faso su fice daga kungiyar kasashe masu amfani da kudaden cfa wato UEMOA bayan kammala wani shirin da ke gabansu a yanzu haka.

Wadanan bayanai na Janar Abdourahamane Tiani na fitowa bainar jama’a ne a wani lokacin da wasu majiyoyi ke cewa Shugaban rikon kungiyar CEDEAO kuma Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya umurci wata tawagga domin zuwa bikon kasashen Nijar, Burkina Faso da Mali su dawo gida.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Shugaban Mulkin Soji Na Nijar Ya Ce Batun Ficewarsu Daga ECOWAS Tabbatacciya Ce.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG