Sakamakon yadda abin ke kawo karshen yanayin kuncin rayuwar da aka shiga yau watanni kusan 7 sanadiyar rufe iyakoki da takaita zirga-zirga harakokin kasuwanci da tsinke wutar lantarki.
Koda yake wasu na ganin matakin ya zo a makare kasancewar tuni Mali da Bukina Faso da Nijar suka sanar da ficewa daga kungiyar ta ECOWAS, don mayar da hankula ga kungiyarsu ta AES.
A daya gefe kuwa, wasu ‘yan kasar ta Nijar sun bukaci aje zuwa mataki na gaba, ma’ana a gaggauta sallamar hambararren shugaban kasa Mohamed Bazoum da maidakinsa, sannan lokaci ya yi da ya kamata hukumomin mulkin sojan Nijar su fitar da jadawalin ayyukan gwamnatin rikon kwarya don bai wa ‘yan siyasa damar soma shirye-shiryen zaben dimokradiya.
Kamfanoni da dama sun tafka asarar dimbin kudade a sanadiyar takunkumin da CEDEAO ko ECOWAS ta kakaba wa Nijar, saboda haka wasu ‘yan kasa ke fatan ganin an fara maganar biyan diyya.
Kawo yanzu mahukuntan jamhuriyar ta Nijar ba su bayyana matsayinsu ba dangane da shawarwari da taron na Abuja ya tsayar.
Dandalin Mu Tattauna