Haka kuma majalisar ta bada amincewar ta dan gane da tsare tsare da ka’idojin da za’a bi wajan hako ma’adanai a kasar ta yadda gwamnati ko ‘yan kasuwa masu zaman kansu zasu hada karfi da karfe domin tabbatar da an yi tsarin da kasar zata sami cin moriya domin janyewa daga ci gaba da dogara akan man fetur da darajarsa ta fadi warwas a duniya.
Malam Garba Shehu, kakaki a majalisar ya bayyanawa wakilin sashen Hausa na muryar Amurka Umar Frauk Musa, cewa “akwai bankin duniya wato World Bank, da kuma bankin ci gaba na kasar Sin wato China, da kuma bankin Islama dake Saudiyya, duk zasu bada gudummuwar basussuka da kuma aikace aikace da zasu yi na raya kasa.”
Ya kara da cewa “yanzu kamar abubuwan da suka faru a Arewa maso gabashin Najeriya na boko haram, akwai bukatar sake gina yankin, haka kuma matsalar cutar shan inna ko Polio, da ta sake kunno kai, akwai bukatar a sake yiwa duk yaran kasar allurer rigakafin cutar, domin kudin da aka ware na kasafin kudi baza su is aba, akwai kuma ayyukan titin jirgin kasa da sauransu”.
Da yake amsa tambayar da wakilin sahsen Hausa ya yi masa akan bashin da ake bin kasarn kakain ya bayyana cewa wannan sabuwar gwamnatin ba kamar gwamnatocin da suk shude bane, wadanda ke amso bashi su kasa kowa ya kwashi rabonsa, kuma akwai kasashen da tattalin arzikin su bai kai karfin na Najeriya ba amma suna karbar bashin da ya linka wanda Najeriya zata amsa.
Ga rahoton rahoton Umar Faruk Musa.
Your browser doesn’t support HTML5