WASHINGTON, D. C. - A wata yarjejeniyar da ta tserar da tsayawar ayyukan gwamnati na dan wani lokaci a cikin watan nan da ake ciki, a cewar kakakin Majalisar wakilan Amurkan Mike Johnson.
Johnson wanda dan jam’iyar Republican ne, ya bayyana cikin wata wasika da ya aikewa ‘yan Majalisar Dokokin, cewa, gagarumin adadin ya hada da dala biliyan 886 da zai je ga bangaren tsaro, sai dala biliyan 704 na ayyukan da basu shafi tsaro ba.
Tun a watan jiya ne dai kudurin kasafin kudin na tsaro ya sami rattaba hannun Shugaba Joe Biden inda kudurin ya zama doka, bayan kare yadda za’a kashe kudaden tsaron.
Wata sanarwar hadin guiwa da shugaban masu rinjiya a Majalisar Dokoki, dan jama’iyar Democrat Chuck Schumer da Shugaban ‘yan jama’iyar Democrat a Majalisar wakilai Hakeem Jeffries suka fitar, tace, kudaden da za’a kashe a bangarorin da basu shafi tsaron ba, zasu kula ne da muhimman bangarori kamar na hakkokin tsofaffin ma’aikatan da suka manyanta, sha’anin kiwon lafiya, da tallafin abinci mai gina jiki, daga kudaden da ‘yan jama’iyar Republican suka nemi a daddatse.