A yau Talata Amurkawa suke kada kuri’unsu a zaben rabin wa’adi, wanda zai fayyace ko ‘yan Democrat za su ci gaba da rike kankanin rinjayen da suke da shi a majalisar ko akasin haka.
Ga karin bayani a fassarar rahoton Arash Arabasadi, wanda Mahmud Lalo ya hada mana.
‘Yan Democrat ne suke da kankanin rinjaye a duka majalisun dokokin Amurka a yanzu, idan kuma za a bi tarihi, akwai yiwuwar jam’iyyar Shugaba Joe Biden ta rasa kujerunta a majalisar wakilai da ta Dattawa, wanda hakan zai sa Republican ta karbe shugabancin majalisun biyu.
Su dai ‘yan Democrat sun ce hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke a farkon shekarar nan, wanda ya haramta zubar da juna biyu, shi ne zai zaburar da masu kuri’a su nufi rumfunan zaben, a gefe guda kuma, matsalar hauhawar farashin kayayyaki na addabar Amurkawa.
“Duk da cewa tattalin arzikinmu na cikin wani mawuyacin hali, wannan ce jam’iyyar ce da take kare hadin kanmu. Wannan ce jam’iyyar da take kokarin saukaka farashin magunguna da samar da inshorar lafiya mai rahusa. Kazalila, wannan ce jam’iyyar da take kokarin kare ‘yancin dan adam da kare jikinka. Saboda haka, ina wannan zabe ne mai matukar sarkakiya. Zabe ne na rabin wa’adi, amma ina da kwarin gwiwar za mu ci gaba da rike rinjayenmu a majalisar Dattawa.” In ji Sanata Cory Booker, dan jam’iyyar Democrat a majalisar Dattawan kasar.
Wasu daga cikin ‘yan takarar da ke neman kujerun majalisar karkashin jam’iyyar Republican, sun fi karkata hankulansu ne kan yadda sahihancin zaben zai kasance, inda suke ta nanata ikirarin tsohon shugaban kasa Donald Trump, wanda ba tare da wata hujja ba, yake cewa an tafka magudi a zaben 2020.
A dalilin haka, cibiyar Carter Center da ke jihar Atlanta, wacce tsohon shugaban Amurka Jimmy Carter da mai dakinsa Roslynn suka kafa – ta tashi haikan wajen horar da masu sa ido kan zabe, kan yadda za su bibiyi yadda zaben zai gudana a karamar hukumar Fulton a jihar Georgia, wacce ta zamanto daya daga cikin jihohin da ‘yan takarar kujerar sanata suke fafatawa.
Dan takarar Democrat kuma Pastor Raphael Warnock shi zai kara da tsohon dan wasan kwallo Herschel Walker a zaben jihar ta Georgia da kowa ya sakawa ido.
“Amurkawa na kara nuna alamun rashin amincewa da yadda zabe ke gudana, hakan ya sa muka ga ya dace a samu masu sa ido wadanda ba ruwansu don su bi diddigin al’amura, da zimmar ganin mun karawa mutane fahimta da samun kwarin gwiwar al’amuran zabe.” David Carroll, jami’i a cibiyar ta Carter Center ya ce.
A can jihar Pensylvania kuwa, ‘yan Democrat ne suka fara ganin haske, yayin da takarar kujerar sanata ta yi zafi tsakanin dan Democrat Laftanar John Fetterman da Dr Mehmet Oz da ke samun goyon bayan Trump ta yi zafi.
Biden dai ya fadawa manema labarai a San Diego cewa, yana da kwarin gwiwa, jam’iyyarsu ta democrat ce za ta lashe zaben, amma kuma ‘yan Republican, sun ce, sun fi hangen nasara.
“Wannan zabe zai zama wa Shugaba Biden hannunka mai sanda, ina fata zai farga, saboda abubuwan da suka faru cikin shekaru biyu da suka gabata, sun haifar da matsaloli da dama a Amurka. Ina fata Biden zai ga yadda Amurka za su fada masa ranar Talata cewa, ba sa jin dadin mulkinsa. Kuma ina ganin, majalisun dokokin Amurka karkashin ragamar ‘yan Republican za su yi aiki tukuru don cika alkawuran da suka yi, ina kuma fata Biden zai saurara.” Glenn Younkin, gwamnan jihar Virginia wanda dan Republican ne ya ce.
Tuni dai rahotanni suka ruwaito cewa sama da mutum miliyan 40 har sun riga sun kada kuri’unsu a damar da ake bai wa ‘yan kasa masu uzuri su yi zabe da wuri tun kafin ranar zabe.