Kwamitin da ke binciken kutsen da aka yi a ginin majalisar dokokin Amurka a ranar 6 ga watan Janairun 2021, ya kada kuri’ar amincewa da aika takardar gayyata ga tsohon Shugaba Donald Trump don ya ba da bahasi.
Kwamitin ya yanke wannan shawara ne bayan da zaman kwamitin wanda mai yi wa shi ne na karshe, ya fayyace cewa akwai bukatar a gayyaci Trump don a ji ta bakinsa game da mamaye ginin majalisar da magoya bayansa suka yi.
Zaman wanda aka yi a jiya Alhamis har ila yau ya yi nuni da irin gagarumar rawa da ake zargin Trump ya taka a yunkurin ganin an sauya sakamakon zaben 2020 wanda Shugaba Joe Biden ya lashe.
Trump da magoya bayansa sun yi watsi da wannan bincike da kwamitin ke gudanarwa, wanda suka kwatanta a matsayin bi-ta-da-kullin siyasa.
Sai dai shugaban kwamitin binciken, Bennie Thompson, ya ce wani abin mamaki shi ne, mafi aksarin bahasin da hujjoji da aka gabatar a binciken daga ‘yan Republicans ya fito.