WASHINTON, D. C - Jami’an soji sun kwace mulki a ranar 30 ga watan Agusta, inda suka soke zaben da aka kammala ‘yan mintoci bayan sanarwar cewa Shugaba Ali Bongo ne ya sake lashe zaben, zaben da suka ce bai inganta ba. Bongo wanda ke kan karagar mulki tun shekara ta 2009 ya gaji mahaifinsa Omar Bongo wanda shi kuma ya shafe shekaru 42 yana mulki.
Jama’ar kasar sun yi na'an da juyin mulkin cikin farin cikin suka nuna murnar su a Libreville babban birnin kasar, kuma a ranar 4 ga watan Satumba alkalai suka rantsar da Janar Brice Oligui Nguema a matsayin shugaban rikon kwarya, inda ya yi alkawarin cewa za'a gudanar da sahihan zabuka cikin 'yanci da adalci, amma bai bayar da ainihin lokacin shirya su ba.
Wakilin musamman na Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya a Afirka ta Tsakiya Abdou Abarry, ya samu ganawa da Nguema a Libreville a ranar Laraba inda ya shaida masa cewa Majalisar Dinkin Duniya za ta taimaka wa kasar yayin da ta fara wani sabon babi.
“Da zarar mun san shirin da kuka yi, yanayin lokaci, da lokacin nada gwamnati, hukumominmu daban-daban za su yi tuntuba don su ci gaba da tallafa wa Gabon,” in ji shi bayan ganawar tasu, a wani jawabi da aka watsa a gidan talabijin na Gabon 24.
Ba kamar Nijar ba, ‘yan kasar Gabon ba su nuna kyama ga Faransa ko nuna daukaka ga Rasha ba, kuma manyan hafsoshin sojin da ke Libreville sun nuna a shirye suke domin tattaunawa da kungiyoyin kasa da kasa, inda takwarorinsu na Yamai su suka yi watsi da hakan.
Kungiyar kasashen Afrika ta tsakiya ECCAS ta dakatar da kasar Gabon a ranar Litinin, amma ta tura shugaban kasar Afrika ta tsakiya Faustin-Archange Touadera a matsayin wakilinta domin ganawa da Nguema.
Touadera ya shaida wa manema labarai cewa ya kuma samu ganawa da Ali Bongo, da izinin Nguema. Bai bayyana wani cikakken bayani game da halin da Bongo ke ciki ba ko kuma halin da ake ciki ba, yana mai cewa taron ya yi tasiri.
Bongo ya kasance cikin daurin talala bayan juyin mulkin, sai dai a wata sanarwa da Gwamnatin mulkin soji ta fitar a ranar Larabar da ta gabata ta ce yanzu yana da 'yanci kuma yana iya tafiya kasar waje domin duba lafiyarsa idan ya so.
-Reuters