MDD Ta Yi Allah Wadai Da Bulala Da Aka Yi Wa Wasu Mutane a Bainar Jama'a A Afghanistan

Jami'an Taliban

Kimanin mutane 63 ne aka yi musu bulala a bainar jama'a a lardin Saripul da ke arewacin kasar a ranar Talata, kamar yadda tawagar Majalisar Dinkin Duniya a Afghanistan (UNAMA) ta sanar.

Majalisar Dinkin Duniya a ranar Laraban da ta gabata ta yi Allah wadai da bulala da aka yi wa mutane da dama a Afganistan, tare da yin kira ga mahukuntan Taliban da su kawo karshen wannan dabi'a.

Kimanin mutane 63 ne aka yi musu bulala a bainar jama'a a lardin Saripul da ke arewacin kasar a ranar Talata, kamar yadda tawagar Majalisar Dinkin Duniya a Afghanistan (UNAMA) ta sanar.

UNAMA chief meeting with Mawlawe Abdul Kabir

"UNAMA ta sake nanata yin Allah wadai da ladabtar da jiki tare da yin kira da a mutunta hakkin dan Adam na kasa da kasa," in ji tawagar a cikin wata sanarwa da aka buga akan shafin X.

Tun bayan dawowar su kan karagar mulki a watan Agustan 2021, hukumomin Taliban sun dawo da wata matsananciyar fassarar shari'ar Musulunci.

Jama'a sun sha kallon yadda ake aiwatar da hukuncin kisa a bainar jama'a da ladabtar da jiki, musamman bulala, galibi kan laifukan da suka haɗa da sata, zina da shan barasa.