WASHINGTON, D.C. - Kawo yanzu dai babu wani da ya dauki alhakin kai harin na daren Laraba, wanda shi ne na baya bayan nan da aka kai a kasar cikin shekara guda tun bayan da 'yan Taliban suka kwace mulki. Rahotanni sun ce yara da dama na cikin wadanda suka jikkata.
Khalid Zadran, kakakin shugaban 'yan sandan Taliban na Kabul ne ya ba kamfanin dillacin labarai na Associated Press alkaluman harin na masallacin Siddiquiya da ke unguwar Kher Khanna na birnin. Wani ganau ya shaidawa AP cewa wani dan kunar bakin wake ne ya tayar da bam din.
Mayakan kungiyar IS sun kara kaimi wajen kai hare-hare kan 'yan Taliban da fararen hula tun bayan da Taliban ta karbe iko a watan Agustan bara a daidai lokacin da dakarun Amurka da na NATO ke matakin karshe na janyewarsu daga kasar.
A makon da ya gabata, masu tsattsauran ra'ayi sun dauki alhakin kashe wani fitaccen malamin Taliban a cibiyar addininsa da ke birnin Kabul.
-AP