Yau Talata Taliban ta ba da umarni dakatar da duk wasu ayukan Sweden a Afghanistan saboda kona Alkur'ani mai girma, da aka yi a bainar jama’a a wata zanga-zanga da aka yi a Sweden a watan da ya gabata.
Zanga-zangar da aka ba da izini a ranar 28 ga watan Yuni ta nuna yadda wani dan kasar Iraqi da ke zaune a Stockholm ya yaga tare da kona alkur'ani a wajen babban masallacin babban birnin kasar a daidai lokacin da Musulmi suke gudanar da bukukuwan sallar idi a fadin duniya.
Kona Alkur’anin dai ya haifar da bacin rai da tofin Allah tsine a kasashen Musulmi, da kuma bore daban-daban daga masu tsatstsauran ra’ayi, sannan ya yi sandiyar mahawara a kasar ta Sweden game da iyakar fadin al’barkacin baki.
Daular ta Islama ta dakatar da ayukan Sweden a Afghanistan saboda ba da iznin cin zarafin Kur’ani da kuma addinin Musulinci,” in ji Taliban, ta hanyar amfani da sunan gwamnatin a hukumace a Kabul.
Dandalin Mu Tattauna