Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Kunar Bakin Wake Ya Kashe Mutane 19 A Kabul


Fashewar Bom A Kabul
Fashewar Bom A Kabul

An kai wani mummunan harin kunar bakin wake a wani dakin karatu da ke cike da dalibai a Kabul babban birnin kasar Afghanistan da sanyin safiyar ranar Jumma’a, wanda ya yi sanadiyyar kisan akalla dalibai 19 kana ya raunata wasu 27. Cikin wadanda lamarin ya shafa har da 'yan mata.

Wadanda suka shaida lamarin da jami’an ‘yan sanda sun ce harin bom din ya faru ne a cikin cibiyar ilimi ta Kaaj da ke yammacin Dash-e-Barchi a birnin Kabul, unguwar da galibi mabiya Shi’a na Hazara ke zama.

Khalid Zadran, mai magana da yawun ‘yan sandan Kabul, ya tabbatar wa VOA rayukan da aka rasa tare da yin tir da tashin hankalin. Ya kuma ce jami’an tsaron Taliban sun isa yankin kuma an fara gudanar da bincike.

Zadran ya ce daliban na shirye-shiryen jarabawar shiga jami’a ne a lokacin da wani dan kunar bakin wake ya kai hari a cibiyar ilimin. Abin takaici, mutane 19 aka kashe sannan wasu 27 suka ji rauni, a cewarsa.”

Wadanda suka tsira da daga harin sun shaida wa kafafen yada labaran kasar cewa akwai dalibai maza da mata 400 a ajin da aka raba tsakaninsu da labule bisa ga umurnin Taliban, da ke rubuta jarabawar shiga jami’a ta gwaji a lokacin da dan kunar bakin waken ya afka musu.

Wani jami’in cibiyar ilimi ta Kaaj da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa VOA cewa akalla dalibai 25 suka mutu, kana wasu 35 suka ji rauni.

Nan take dai babu wanda ya dauki alhakin kai harin bom din.

XS
SM
MD
LG