Taliban ta ce ofishin jakadancin Afghanistan dake Indiya zai maido da aikace aikacen shi nan ba da jimawa ba. Yunkurin hakan ya biyo bayan da jami’an diplomasiyya dake biyayya ga gwamnatin kasar da aka tsige da Amurka ke marawa baya, ta bayyana a makon jiya cewa, zasu rufe ofishin jakadancin har illa ma sha Allahu.
Wani babban jami’in gwamnatin Taliban ya bayyana cewa, wakilan su, sun karbi ragamar ayyukan diplomasiyyar Afghanistan a kasar ta Indiya, da ya hada da ofishin jakadancin dake New Delhi.
Mataimakin ministan harkokin waje na Taliban, Shir Mohammad Abbas Stanekzai, ya shaidawa kafar Talabijin din kasar ta Afghanistan cewa, a nan da yan kwanaki masu zuwa ne za a sake bude ofishin jakadancin dake babban birnin kasar ta Indiya.
Furucin mataimakin ministan ya zo ne, bayan da jami’an diplomasiyya dake biyayya ga gwamnatin kasar da aka tsige da Amurka ta marawa baya, ta bayyana a makon jiya cewa, za ta rufe ofishin jakadancin na din din din, bisa zargin rashin hadin kai daga kasar, da ma sauran wasu dalilai.
Stanekzai ya fada cikin wata hira da aka yi da shi ta kafar Talabijin din RTA aka yada ta a ranar Talata, cewa, karamin ofishin jakadancin Taliban dake Mumbai da Hyderabad na aiki bisa tuntuba da ma’aikatar harkokin waje dake Kabul, da gudanar da ayyuka na yau da kullum kamar yadda aka saba.
Ya kara da cewa, a farkon makon nan ne ayyukan ofisoshin jakadancin ya koma birnin New Delhi, aka kuma sake bude ofisoshi a ofishin jakadanci dake Afghanistan. "Don haka in Allah ya yarda, ofisoshin jakadancin mu zasu koma aiki gadan gadan nan da kwanaki biyu zuwa ukku’’.
Taliban dai ta sake darewa kan karagar mulki ne a Afghanistan shekaru biyu da su ka gabata, amma a lokacin kasar Indiya da sauran kasashen duniya basu aminta su kulla wata huldar diplomasiyya da su ba, akasari bisa dalilan keta haddin bil’adama da tsananin da suke nunawa ga mata a kasar ta Afghanistan.
A ranar Juma’ar da ta gabata ofishin jakadancin Afghanistan ya wallafa wata sanarwa a shafin X da aka fi sani da Twitter a baya, cewa za’a rufe ofishin, a kuma mika makullan ga gwamnatin Indiya. Tayi zargin matsin lamba daga bangarorin biyu, Indiya da Taliban ya tilasta daukar matakin.
Dandalin Mu Tattauna