Majalisar Dinkin Duniya Ta Ce Mutane Miliyan 8 Na Bukatar Abinci Cikin Gaggawa A Yankin Kudu Maso Gabashin Afirka

  • Ibrahim Garba

Wasu kayan abinci

Hukumar Samar da Abinci Ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane sama da miliyan 8 ne ke bukatar taimakon gaggawa na abinci a kasashen gudu maso gabashin Afirka.

Hukumar Samar da Abinci Ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane sama da miliyan 8 ne ke bukatar taimakon gaggawa na abinci a kasashen kudu maso gabashin Afirka.

Hukumar ta abinci da noma (FAO a takaice), ta yi gargadi jiya Talata cewa ana bukatar kayan abinci a Djibouti da Habasha da Kenya da kuma Somaliya cikin gaggawa.

Hukumar ta ce kasashen sun yi fama da karancin ruwa na tsawon shekaru biyu a jere, wanda hakan ya haddasa fari da asarar dabbobi da abincin dabbobin.

Saboda karancin abincin, jami’an Majalisar Dinkin Duniya sun ce matsalolin da ke da nasaba da rashin abinci mai gina jiki ta ta’azzara a yankin. Sun ce mai yiwuwa matsalar ta kara tsananta saboda fari na ta faruwa akai-akai.

Hukumar ta ce dole fa ne manoma da makiyaya su yi damarar fuskantar yanayi mai tsananin muni.