Shugabannin arewaci da kudancin Sudan sun shiga kwana na biyu na tattaunawa a yunkurin shawo kan takaddamar da ake yi a kan iyakarsu kafin kudanci ya wanzar da cin gashin kai watan gobe. Shugaban arewacin Sudan Omar al-Bashir da takwaransa na kudanci Salva Kiir suna tattaunawa tare da masu shiga tsakanin na KTA a Addis Ababa babban birnin kasar Habasha. Jiya Lahadi majiyu dake kusa da taron suka ce Mr. Bashir ya amince da janye dakarun arewacin kasar da suka mamaye yankin Abyei mai arzikin man fetir da ake takaddama a kai. Yarjejeniyar da ake neman kullawa zata kunshi tura dakarun kiyaye zaman lafiya na kasar Ethiopia a kan iyakar kasashen da ba a riga a shata ba. A cikin sanarwar da ta bayar daga Tanzaniya yau Litinin sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton tace Amurka tana son ganin an janye dakarun arewacin daga Abyei, zata kuma yi na’am da tura dakarun kiyaye zaman lafiya na kasar Habasha a yankin.
Shugabannin arewaci da kudancin Sudan sun shiga kwana na biyu na tattaunawa a yunkurin shawo kan takaddamar da ake yi a kan iyakarsu kafin kudanci ya wanzar da cin gashin kai watan gobe.