Fiyeda kasashe 30 ne ciki har da Amurka suka amince da gwamnatin wucin gadi ta ‘yan tawaye a Libya, suna masu ikirarin cewa shugaban kasar Moammar Gadhafi, bashi da sauran halaccin iko kan kasar dake arewacin Afirka.
A yau jumma’a ce kasashen yammaci da na yanki suka bayyana goyon bayan ga nasu a Istanbul, inda suka hallara domin tsara dabaru da hanyoyin karfafa ‘yan atwayen a yunkuri da suke na hambare Mr. Gadhafi daga mulki da yanzu yayi shekaru 42.
Daga bisani cikin wani sako da aka yadawa dubban magoya bayansa a garin Zlitan, Mr. Gadhafi yayi wasi da amincewar da kasashen suka yi wa ‘yan tawayen. Yayi kira ga magoya bayansa kamar yadda yake cewa “ku tattaka ku murkushe wan nan amincewar, sabo da bata da wani tasiri.
Jami’an kwamitin tuntubar sun ce zasu yi mu’amala da majalisar wucin gadin a matsayin halattaciyar gwamnatin Libya,har sai an kafa sabuwar gwamnatin wucin gadin kasar.