Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Arewaci Da Kudancin Sudan Na Gab Da Cimma Maslaha


Wani sojan tabbatar da zaman lafiya a yankin Abyei
Wani sojan tabbatar da zaman lafiya a yankin Abyei

Shugabannin arewaci da kudancin Sudan na gab da cimma masalaha kan janye sojoji daga kan iyakar yankin Abyei da ake takaddama akai kafin kudu ta balle ran 9 ga watan Yuli.

Shugabannin arewaci da kudancin Sudan na gab da cimma masalaha kan janye sojoji daga kan iyakar yankin Abyei da ake takaddama akai kafin kudu ta balle ran 9 ga watan Yuli.

Wakilin Muryar Amurka Peter Heinlein ya bayar da rahoton cewa Shugaban arewaci Omar al-Bashir da na Kudanci Salva Kiir sun fara tattaunawa ran Lahadi a Adis Ababa, babban birnin Ethiopia.

Y ace sun gana da manyan kusoshin kungiyar Tarayyar Afirka das u ka hada da Firayim Ministan Habasha Meles Zenawi da tsohon shugaban Afirka ta kudu Thabo Mbeki. An shirya cigaba da tattaunawar a yau Litini.

Mr. Mbeki ya kuma ce bangarorin biyu na tattaunawa kan yiwuwar girke rundunan tabbatar da zaman lafiya bisa jagorancin kasar Habasha a kan iyakar kudu da arewa.

Dakarun arewa sun mamaye yankin Abyei mai arzikin man fetur a watan jiya, wanda hakan ya sa dubban mutane tserewa daga yankin.

A jiya lahadin kuma, Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya yi kira ga dukkannin bangarorin su daina fada a wurin a sa’ilinda yake maraba da tattaunawar ta Addis Ababa.

A wani al’amarin kuma na dabam dakarun arewa sun cigaba da yakar kungiyoyin mayakan sa kai a jihar kudancin Kordofan da ke kan iyaka yau sama da sati kenan. Ran Lahadi, dakarun arewa sun karyata rahotannin da ke nuna cewa an harbor wasu jiragen yakinsu biyu har kasa a kudancin Kordofan.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG